IQNA

Iran Ta Kirayi Kasashen Musulmi Da Su Kawo Karshen Kisan Gillan Musulman Myanmar

16:26 - October 31, 2012
Lambar Labari: 2441342
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira ga dukkanin kasashen musulmi da kuma kungiyoyi na kasa da kasa da su dau matakan da suka dace sannan kuma cikin gaggawa wajen kawo karshen kisan gillan da ake yi wa musulmin kasar Myammar.


Yayin da ya ke magana kan wannan lamarin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Ramin Mehmanparast ya ce irin danyen aikin da ake tafkawa a kasar Myammar na irin kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar wani lamari ne da a matakin farko yake nuni da rashin gaskiyar ikirarin kasashen yammaci kan kare hakkokin bil’adama. A saboda haka ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce ya zama wajibi a dau matakan gaggawa kuma ba sani ba sabo wajen kawo karshen wannan kisan gillan. Mataimakin shugaban jam’iyyar musulmi ta Muslim National Democratic Party for Development ta kasar Myammar din HlaThein ya bayyana cewar sama da musulmi 100 ne aka kashe a rikicin baya-bayan nan da ya barke a jihar Rakhine na kasar ta Myammar sakamakon hare-haren da mabiya addinin Budha masu tsattsauran ra’ayi suke kai wa musulmin jihar. Gwamnatin kasar Myammar din ta ki ta amince da musulmin Rohingyas din a matsayin ‘yan kasar lamarin da ya ba wa ‘yan Budhan karfin gwuiwan ci gaba da kashe su.
1129143
captcha