IQNA

Shugaban Masar Ya Bai Wa Sojojin Kasar Izinin Kame Fararen Hula Idan Suka Saba Ma Ka'ida

12:46 - December 11, 2012
Lambar Labari: 2461947
Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya baiwa rundunar sojin kasar izinin kame duk wanda ya sabawa doka ko da kuwa farar hula ne a ko’ina cikin fadin kasar.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga birnin Alkahira na kasar Masar ya bayyana cewa, a yau ne shugaba Morsi ya baiwa sojojin kasar ikon kame duk wani mutum koda kuwa farar hula ne da ya sabawa doka. Wannan umurni na shugaban kasar ta Masar ya zo ne a daidai lokacin da masu adawa da sabon kundin tsarin mulkin kasar suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kiyayya da shi a mafi yawan biranan kasar.
Muhammad Morsi ya kara wa kansa karfin iko fiye da wanda dokar shugabancin kasar ta tanadar, lamarin da ya fusata da dama daga cikin magoya bayan jam’iyun adawa, har da wasu daga cikin wadanda suka yi kawance da shi a lokacin zaben shugabancin kasar, lamarin da ke ci gaba da jawo tashe-tashen hankula a kasar.
Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya baiwa rundunar sojin kasar izinin kame duk wanda ya sabawa doka ko da kuwa farar hula ne a ko’ina cikin fadin kasar. Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga birnin Alkahira na kasar Masar ya bayyana cewa, a yau ne shugaba Morsi ya baiwa sojojin kasar ikon kame duk wani mutum koda kuwa farar hula ne da ya sabawa doka. Wannan umurni na shugaban kasar ta Masar ya zo ne a daidai lokacin da masu adawa da sabon kundin tsarin mulkin kasar suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kiyayya da shi a mafi yawan biranan kasar. Muhammad Morsi ya kara wa kansa karfin iko fiye da wanda dokar shugabancin kasar ta tanadar, lamarin da ya fusata da dama daga cikin magoya bayan jam’iyun adawa, har da wasu daga cikin wadanda suka yi kawance da shi a lokacin zaben shugabancin kasar, lamarin da ke ci gaba da jawo tashe-tashen hankula a kasar.

1150864
captcha