Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Syria sun tabbatar da cewa wasu daga sarakunan larabawa suna taimaka yan ta’addan kasar Syria wajen kaddamar da hare-hare kan sansanin palastinwa yan gudun hijira na yarmuk a kusa da birnin Damascus sakamakon kin bayar da hadin kai ga ‘yan ta’addan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa sojojin kasar Syria na ci gaba da fattatkar ‘yan ta’adda daga yankunan da dama da suka kafa tungarsu a cikin lardunan Hamah da kuma Homs gami da Aleppo.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga kasar Syria ya habarta cewa, dakarun na Syria tare da taimakon al’ummar gari, suna ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addan daga wuraren da suke buya, inda a cikin sa’ioi 24 da suka gabata, sojojin na kasar Syria sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda masu dauke da makamai fiye da 27 a yankunan Dair Zur da kuma gefen birnin Hamah, kamar yadda suke ci gaba da fattatar ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare kan sansanin palastinawa ‘yan gudun hijira na Yarmuk.
A jiya ne dai Firaministan kasar Syria Wa’il Halaki ya kai ziyara tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Syria zuwa birnin Aleppo, inda suka gane wa idanunsu irin barnar da ‘yan ta’adda suka yi a garin, da kuma jin koke koken jama’ar birnin.
1155572