IQNA

Larjani Ya Taya takwarorinsa shugabannin majalisun kasashen Kiristo Murna Haifuwar Annabi Isa(AS)

16:41 - December 25, 2012
Lambar Labari: 2470187
Bangaren siyasa: shugaban majalisar dokoki jamhuriyar musulunci ta Iran Ali Larjani a cikin wani sako na taya murna da ya aikewa takwarorin aikinsa shugabannin majalisun dokoki na kasashen kirsitoci ya taya su murnar zagayowar irin wannan rana ta haifuwar annabi Isa (AS).

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: shugaban majalisar dokoki jamhuriyar musulunci ta Iran Ali Larjani a cikin wani sako na taya murna da ya aikewa takwarorin aikinsa shugabannin majalisun dokoki na kasashen kirsitoci ya taya su murnar zagayowar irin wannan rana ta haifuwar annabi Isa (AS).A cikin wannan sakon ya nuna masu muhimmancin wannan rana ga mabiya addinin kirista da kuma sauran takwarorinsu mabiya addinai musamman addinin musulunci da ke girmama sauran annabawa da manzonni da bas u matsayi da girman da Allah y aba su a cikin kur'ani da kuma girma musamman sakon da annabi Isa (AS) ya zo da shi da wasicin da yayi wa mabiya addinin kirista da cewa wani annabi mai suna Ahmadu zai zo bayansa .Har ila yau a cikin sakon yayi fatar ganin mabiya addinin kirista da musulmi sun taimaka wajken fahimtar juna da kawo karshe rikicin da akw fuskanta yau a duniya kasashe daban daban.

1159849
captcha