Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen duniya da dama suna ci gaba da yin kakkausar suka dangane da hukuncin da kotun kolin kasar ta tabbatar kan manyan adawar siyasa na kasar da ake tsare da su gami da wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil adama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen duniya da dama suna ci gaba da yin kakkausar suka dangane da hukuncin da kotun kolin kasar ta tabbatar kan manyan adawar siyasa na kasar da ake tsare da su gami da wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar musamman ma Nabil Rajab daga cikinsu.
Gwamnatin kasar ahrain ta kame daruruwan 'yan siyasa da suke kalu balantarta kuma tana ci gaba da tsare su a tare da wata hujja ba, daga bisani saboda matsin lambar kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya hakan yasa aka gurfanar da su a gaban kuliya kuma aka yanke hukuncin daurin rai da rai a kansu, kamar yadda daga bisani kotun kolin kasar ta kara tabbatar da wannan hukuncin.
Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen duniya da dama suna ci gaba da yin kakkausar suka dangane da hukuncin da kotun kolin kasar ta tabbatar kan manyan adawar siyasa na kasar da ake tsare da su gami da wasu daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.
1169824