Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro da ya hada malaman addini da kuma masana kan harkokin addini da malaman jami’a dangane da ilmomin kur’ani da kuma yadda za a kara fada koyarwarsa atsakanin al’ummar musulmi na kasar Pakistan tare da kokari daga kowane bangare na al’ummar kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a kasar Pakistan an gudanar da wani zaman taro da ya hada malaman addini da kuma masana kan harkokin addini da malaman jami’a dangane da ilmomin kur’ani da kuma yadda za a kara fada koyarwarsa atsakanin al’ummar musulmi na kasar Pakistan tare da kokari daga kowane bangare na al’ummar kasar baki daya.
A wani labarin kuma Kotun kolin kasar Pakistan ta bada umurnin kame fira ministan kasar kan zargin hannu a batun cin hanci da rashawa tare da wasu tsoffin ministocin kasar. Kotun kolin kasar Pakistan a yau Talata ta fitar da warantin kame fira ministan kasar Raja Pervez Ashraf kan zargin hannu a karbar cin hanci a shekara ta 2010 a lokacin da yake rike da mukamin ministan ruwa da makamashi. Har ila yau kotun kolin kasar ta Pakistan ta bada umurnin kame wasu mutane goma sha shida ciki har da tsoffin ministocin kasar guda uku duk dai a kan zargin hannu a karbar cin hanci da rashawa a kasar.
Kotun kolin ta bada kwana daya ne kacal ga mahukuntan kasar kan su mika mata fira ministan da sauran mutanen da ake zargi. Wannan lamari ya fara janyo ka ce na ce a kasar ta Pakistan, kuma har dubban 'yan adawar siyasa sun fara gudanar da taron gangami a birnin Islam-Abad fadar mulkin kasar a yau Talata suna neman rusa gwamnatin Pakistan da Majalisar Dokokin kasar.
1171619