IQNA

Jagoran Juyin Juya Ya Mika Sakon Ta'aziyar rasuwar Hajji Muhammad Ali Auhadi

23:28 - January 19, 2013
Lambar Labari: 2482778
Bangaren siyasa jagoran jiuyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali khamenie ya bayyana kyautata bangaren lafiya da samar da magani wa al'umma a matsayin daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci a kasar Iran, sannan kuma yayin da ya ke jinjinawa irin ayyukan da kungiyar ta yi a wannan fagen ya bayyana cewar: A duk inda imani, karfi da kuma kumaji irin na mutane suka shigo fage, to kuwa albarkoki ninkin ba ninkiya za su shigo cikin ayyuka sannan kuma za a magance matsaloli.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da ya yi a safiyar yau litinin membobin kungiyar ba da agaji a bangaren kiwon lafiya na kasar Iran, ya bayyana kyautata bangaren lafiya da samar da magani wa al'umma a matsayin daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci a kasar Iran, sannan kuma yayin da ya ke jinjinawa irin ayyukan da kungiyar ta yi a wannan fagen ya bayyana cewar: A duk inda imani, karfi da kuma kumaji irin na mutane suka shigo fage, to kuwa albarkoki ninkin ba ninkiya za su shigo cikin ayyuka sannan kuma za a magance matsaloli.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin rawar da mutane suke takawa a dukkan fagage masu muhimmanci da suka hada da siyasa, tattalin arziki, kiwon lafiya, al'adu da kuma ilimi, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Shi kansa juyin juya halin Musulunci ya dogara ne da kasantuwar mutane a fage, matukar kuwa mutane ba su shigo fage ba, to kuwa babu abin da ‘yan siyasa da jam'iyyun siyasa za su iya yi.
Don haka sai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi kira da cewa: wajibi ne jami'an gwamnati da sauran mutane masu kishi su yi wani tsari na bin diddigin matsalolin da ake fuskanta don magance su don mutane su sami kwanciyar hankali.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi karin haske kan muhimmancin da ke cikin kiyaye irin gudummawar da mutane suke bayarwa a irin wadannan kungiyoyi na taimakon inda ya ce: Bai kamata a yi sako-sako da irin rawar da mutane suke takawa a wannan bangaren ba.
A bangaren karshe na jawabin nasa Ayatullah Khamenei ya bayyana ganin kyakkyawan sakamakon irin wadannan ayyukan na taimako a matsayin mafi girman abin da ke karfafa wa wannan bangare na taimako gwiwa, daga nan kuma sai ya ce: Akwai yardar Allah Madaukakin Sarki cikin irin wadannan ayyuka na taimako, sannan kuma duk wani aiki na alheri da taimako yana nan rubuce cikin takardar ayyuka sannan kuma ba za su bace ba.
Tun da farko dai sai da babban sakataren kungiyar taimakon kiwon lafiya na Iran Sayyid Ridha Niri ya gabatar da rahoto kan irin ayyukan da kungiyar ta gudanar da kuma abubuwan da ta sanya a gaba.

1174199
captcha