Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Saud Faisal ya tabbatar da cewa kasar Saudiyya da sauran kasashen larabawa na yankin tekun fasha suna da hannu wajen haddasa rikicin kasar Syria kuma ga dukkanin laamu yana tsoron abin da zai je ya dawo bayan haddasa wannan rikici da suka saboda yana zaton ba za su ci narasa ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin din Al-alam cewa, Ministan harkokin wajen Saudiyya Sa'ud Faisal ya fadi a gaban taron kasashen larabawan yankin tekun fasha da aka kammla jiya Talata a birnin Riyadh cewa: "Mun saka kanmu cikin babbar matsala a Syria, wane ne daga cikinmu ke zaton cewa za mu yi nasara a abin da muke yi a Syria? Inda ya tabbatar da cewa bas u da zaton samun narasa a bin da suke yi wanda ga alama ba shirinsu ba ne, illa dai kawai suna aiwatarwa ne.
Ministan na Saudiyya tare da takwaransa na kasar Qatar Hamad Bin Jasim sun yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakan gaggawa na shigar da sojojinta cikin kasar Syria domin yakar gwamnatin kasar tare da kawo karshenta ta yadda hakan zai ba su damar samun cimma nasarar da suka kasa cimmawa tsawon watanni ashirin da biyu a kasar.
Da dama daga cikin masana dai sun bayyana furucin na Saud faisal da cewa alama c eta karaya ta fara bayyana daga mahukuntan Saudiyya kan ramin da suka haka kuma suka fada acikinsa a kasar Syria, wanda kuma uwar gijiyarsu Amurka ba a shirye take ta ci gaba da kare su kan hakan ba.
1176602