IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Ce Fahimta Da Yin Aiki Da Koyarwar Manzon Allah (SAW) Ita Ce Mafita

23:26 - January 25, 2013
Lambar Labari: 2485801
Bangaren kasa da kasa, bababn sakataren kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullan ya bayyana cewa muslmi suna fuskantar babban makirci daga makiya musamman yahudawan sahyuniya da suke tsananin gaba da addinin muslinci da muslmi a duniya baki daya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Almanar cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, babu banbancin manufa a tsakanin dukkanin bangarorin siyasar haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummomin larabawa da musulmi. Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a wani jawabi dazun nan a birnin Beirut a taron maulidin manzon Allah, wanda aka nuna kai tsaye a allunan talabijin, ya ce yadda zaben ya gudana a haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin makon nan ya tabbatar da cewa akwai babbar matsalar siyasa a tsakanin manyan jami'an haramtacciyar kasar, amma kuma a lokaci guda hakan ba ya nufin cewa akwai banbanci a tsakaninsu kan yadda suke kallon musulmi da larabawa a matsayin manyan makiyansu. Sayyid nasrullah ya jadda cewa babban abin da ke gaban musulmi shi ne fahimtar hakikanin koyarwar manzon Allah da kuma yin aiki da wannan koyarwar a cikin dukkanin bangarorin rayuwarsu, domin kuwa wannan shi ne hakikanin addinin muslunci wanda makiyansa ke hankoron ruwa, ta hanyar cin zarafin wannan manzo mai madaukakin matsayi da daraja, kamar dai yadda duniya take shedawa a halin yanzu.

1177404


















captcha