Kamfanin dilancin labaran labaran iqna ya habarta cewa, bababn malamin addinin muslunci na kasar Australia sheikh Abdullah Hilali ya bayyana cewa daya daga cikin manyan malaman da suka halarci taron hadin kan al'ummar musulmi na kasa da kasa a birnin Tehran ya bayyana cewa babban mataki na hada kan al'ummar musulmi shi ne yaki da tunanin kafirta sauran musulmi da wasu masu gurbatacciyar akidar musulucni suke yi a matsayin suna addini na gaskiya.
A daren jiya ne aka kawo karshen taron kasa da kasa kan hadin kan al'ummar musulmi karo na ashirin da shida na kwanaki biyu da aka gudanar da shi a nan Tehran inda aka kafa kungiyar hadin kan malamai 'yan gwagwarmaya da cibiyar tattaunawa tsakanin mazhabobin Musulunci da nufin ci gaba da bin diddigin lamurran da suka shafi hadin kan al'ummar musulmi.
A bayanin bayan taron da aka karanta a daren jiya, mahalarta taron sun yi kiran da a magance matsalolin da kasashen musulmi suke fuskanta musamman lamarin kasar Siriya cikin ruwan sanyi da hanyoyi na siyasa, kamar yadda kuma suka yi kiran da a kawo karshen zubar da jinin musulmi da ake yi a kasashe daban-daban.
Har ila yau a yayin taron, manyan malaman Musulunci da suka halarci taron sun fitar da wata fatawa da haramcin jinin duk wani mutumin da ya yi imani da kalmar shahada, kamar yadda kuma malaman suka yi Allah wadai da kuma haramta duk wata fatawar da ke haifar da fitina a tsakanin musulmi.
A safiyar yau ne ake sa ran mahalarta taron za su gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a gidansa da ke nan Tehran.
1179603