IQNA

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Nuna Damuwa Kan Kisan Musulmin Mali

23:21 - January 29, 2013
Lambar Labari: 2488175
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinin duniya ya nuna matukar damuwa dangane da kisan musulmi da ake yi a kasar Mali da sunan yaki da ta'addanci wanda faransa ta shiga gaba wajen aiwatar das hi wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Afirk cewa, Ban Ki Moon babban sakataren majalisar dinin duniya ya nuna matukar damuwa dangane da kisan musulmi da ake yi a kasar Mali da sunan yaki da ta'addanci wanda faransa ta shiga gaba wajen aiwatar das hi wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama da suka hada da mata da kanan yara.

A daidai lokacin da sojojin kasar Mali da na Faransa suke ci gaba kai hare-hare da kwato garuruwan arewacin kasar da ke hannun 'yan tawaye, babbar mai shigar da kara a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka Fatou Bensouda ta ja kunnen jami'an kasar Mali dangane da rahoton da ke cewa sojojin kasar suna ci gaba da cin zarafin mutane a kasar musamman a garuruwan da suka kwace.

A cikin wata sanarwa da babbar mai shigar da karar ta fitar daga helkwatar kotun da ke birnin Hague na kasar Holland, ta bayyana cewar: ofishinta yana sane da labarin da ke cewa akwai yiyuwar sojojin Malin sun gudanar da ayyukan take hakkokin bil'adama a garuruwan tsakiyar kasar, don haka sai ta kirayi gwamnatin kasar Malin da ta gaggauta kawo karshen hakan da kuma gudanar da bincike kan wannan zargin da kuma hukumta wadanda suke da hannu cikin hakan.

A makon da ya wuce ne hukumar kula da hakkokin bil'adama na kasa da kasa (FIDH) ta yi zargin cewa sojojin kasar Malin sun bindige wasu mutane a arewacin kasar Malin bayan da suka sami nasarar kutsawa wasu garuruwan arewacin biyo bayan harin da sojojin kasar Faransa suka kaddamar a kan 'yan tawayen kasar da nufin kwato arewacin kasar daga hannunsu.

1179779











captcha