Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Aytaollah Sayyid Ali Khamenei ya kai wata ziyara a hubbaren marigayi Imam Khomeini da ke birnin Tehran a daren fara tarukan tunawa da zagayowar ranakun juyin juya halin muslunci a Iran wanda marigayin ya jagoranci kafawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya kai wata ziyara a hubbaren marigayi Imam Khomeini da ke birnin Tehran a daren fara tarukan tunawa da zagayowar ranakun juyin juya halin muslunci a Iran wanda marigayin ya jagoranci kafawa shekaru 34 da suka gabata.
A yau Alhamis ne za a fara bukukuwan zagayowar ranakun cin nasarar juyin musulunci a duk fadin Iran. Shugaban hukumar da ta ke kula da shirya bukukuwan cin nasarar juyi, Muhsin Sabbag, ya fada a yau laraba cewa; a gobe alhamis ne za a bude kan bikin na tunawa da ranakun cin nasarar juyi a hubbaren marigayi Imam Khumain (r.a), wanda zai sami halartar bangarori daban-daban na al'umma. Sabbagh ya kara da cewa; da akwai shirye-shirye na musamman da aka tsara za a aiwatar domin tunawa da shiowar lokacin da Imam Khumaini ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Mehrabad.
Da akawi kuma ayarin baburan 'yan sanda da za su tashi daga filin saukar jiragen na Mehraabd tare da yin ruwan furanni da kuma kabbarori a cikin masallatai da kuma kada karaurawar majami'oi. A rana irin ta gobe 12 ga watan Bahman ne dai jagoran juyin musulunci na Iran Ayatulah Imam Khumaini ya dawo Iran bayan shekaru 15 na gudun hijira.
1180133