Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tshar Al-alam cewa, sheikh Badrudddini Hassun babban malamin addainin muslunci akasar Syria ya bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra'ila tana da hannu a cikin dukaknin rikicin da yake faruwa akasar wanda a halin yanzu harin da ta kai kan kasar ya tabbatar da cewa babu mai shakku kan hakan ga mai shakku.
Rahotanni daga kasar Syria sun habarta cewa, dakarun kasar sun hallaka 'yan bindiga 70 a yau a ynkin Shabibah da ke cikin gundumar Idlib a gabacin kasar, biyo bayan musayar wutar da suka yi a lokacin da maharan suke kokarin kutsawa wani wurin tsaro dauke da muggan mkamai da suka fito da su daga kasar Turkiya.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga yankin ya bayyana cewa, maharan sun nufi wurin da nufin kwace daga hannun dakarun gwamnatin Syria, amma sojojin na Syria suka yi musu kwantan bauna, inda suka kashe su baki dayansu, daga cikin maharani hard a Abu Walid Ahmad Bakir, daya daga cikin fitattun jagororin 'yan tawayen Syria, wanda ya jagorancikai hare-hare da dama a yankin Idlib, da suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan fararen hula.
A bangare guda kuma a yau ne babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Said Jalili ya isa birnin Damascus an kasar Syria, inda yake ganawa da manyan jami'an kasar dangane da halin da ake ciki, da kuma irin gudunmawar da Iran take bayrwa domin ganin an kawo karshen rikicin na kasar Syria, wanda kasashen yammacin turai suka haddasa tare da taimakon wasu daga cikin kasashen larabawa na yankin, saboda wasu manufofi na siyasa.
1181001