IQNA

A yau ne ake gudanar da janazar shugaban tawagar injiniyoyi Iraniyawa a Lebanon Husam Khusnavis

23:20 - February 15, 2013
Lambar Labari: 2496729
Bangaren kasa da kasa, A yau ne ake gudanar da janazar shugaban tawagar injiniyoyi Iraniyawa a Lebanon Hda ke gudanar da ayyukan sake gina yankunan da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta rusa a lokacin yakin shekara ta 2006 a kasar Lebanon bayan da wasu mutane dauke da makamai suka kai masa hari a daren laraba da ta gabata a kan hanyarsa ra komawa Beirut daga Syria.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na presstv cewa, a yau ne ake gudanar da janazar shugaban tawagar injiniyoyi Iraniyawa a Lebanon Hda ke gudanar da ayyukan sake gina yankunan da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta rusa a lokacin yakin shekara ta 2006 a kasar Lebanon.

Ofishin jakadancin kasar Iran a birnin Beirut ya sanar cewa wasu ma'aikatan haramtacciyar kasar Isra'ila ne suka yi ma Husam Khusnavis kisan gilla a daren Larabar da ta gabata a lokacin da yake kan hanyarsa ta isa birnin Beirut, bayan ya dawo daga kasar Syria, kuma a yau ne za a gudanar da janazarsa a birnin Simnan mahaiarsa da ke Iran.

Tuna cikin shekara ta 2006 bayan kawo krashen yakin da haramattacir kasar Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Lebanon, injiniya Husam yake jagorantar tawagar injiniyoyi Iraniyawa da suke gudanar da aikin sake gina wuraren day akin ya daidaita, da hakan ya hada da dubban gidajen jama'a, daruruwan masallatai da cibiyoyin addini da na kiwon lafiya gami da makarantu.

1188839






captcha