Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Bahrain sun habarta cewa lamurra sun tsaya cak a kasar, sakamakon zanga-zangar da al'ummar kasar ke gudanarwa domin tunawa da cika shekaru biyu da suka fara bore na lumana domin neman gyara acikin harkokin mulki da siyasar kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni suka ce an rufe dukkanin kasuwanni da masana'antu har ma da wasu daga cikin muhimamn wuraren gwamnati, da suka hada da babban filin safka da tashin jiragen sama na birnin Manama, sakamakon jerin gwanon da ake yi a ko'ina cikin fadin kasar.
Al'ummar kasar Bahrain sun fara zanga-zangar neman hakkokinsu na siyasa a matsayinsu na 'yan kasa ne a ranar 14 ga watan Fabrairun shekara ta 2011, inda suka bukaci maarautar kasar da ta ci gaba da mulki, amma a baiwa al'ummar zabar mambobin majalisar dokoki da kansu, maimakon sarki ya nada wadanda ya ga dama ba tare da ra'yin al'umma ba.
Maimakon sauraren kiran da al'ummar kasar suke yi, gidan sarautar Bahrain ya nemi taimakon gidan sarautar Saudiyya domin murkushe fararen hula da ke jerin gwano na lumana a kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, sakamakon yin amfani da karfi da jami;an tsaron kasar da Saudiyya suke yi, kammar yadda yanzu haka ake tsare da daruruwan muatane da aka kame bisa zarginsu da nuna kiyayya ga gidan sarauta.
1188818