IQNA

An soki lamirin masu taimaka ma ‘yan tawayen Syria da fatawowyi na kafirta musulmi

17:07 - February 16, 2013
Lambar Labari: 2497356
Bangaren kasa da kasa, halin da ake ciki a rikicin kasar Syria yana nuna cewa har yanzun ba'a sami damar yentar da mutanen da wasu yan bindaga suka yi garkuwa da su a ranar Alhamis da ta gabata, sannan sojojin kasar Syria sun yi muwafakar kashe yan ta'adda da dama a yankuna daban daban na kasar, sannan akwai labarai da suke nuna cewa ana kara samun sabani a cikin yan ta'addan kasar ta Syria da kuma shirye shiryen gwamnatin kasar na shiga tattaunawa tare da dukkan bangarorin mutanen kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba'a gano ko suwaye ne ba, suka yi garkuwa da mutane kimani 100 da ke cikin wasu motocin bus bus guda 4 dauke da yara mata da maza a unguwannin Al-Fure , da Kufuryo a garin Idlib na kasar Syria. Yan bindigan sun yi alkawarin sake wadan nan mutane amma har yanzun basu cika alkawarin nasu ba.
Wasu dangin wadanda aka yi garkuwa da sun, sun zargi yan bindigan da rashin ciki alkawarin da suka yi na sakin su, da nufin haddasa rikici a kasar Syria. Har'ila yau yana daga cikin labarunrikicin kasar Syria cewa sojojin kasar sun sami nasarori da dama a kan yan ta'adddar kasar a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka kashe da dama daga cikinsu a garuruwan Halab, Aziziyya, Kufur-Hamraa da kuma Al-Baab, sannan wasu da dama kuma suka sami raunuka. Wani labari dangane da rikicin kasar ta Syria shi ne karuwan sabani tsakanin yan ta'adan kasa.
Tariq Al-Ahmad wani dan "jam'iyyar mutanen Syria" ya ce sanarwan da shugaban yan ta'addan kasar ta Syria Mu'az Al-khadib ya bayyana na shiga tattaunawa da gwamnatin kasar Syria ya kara raba kan yan adawar kasar ta Syria ya kuma maida su bangare bangare. Hakama, sabani da rashin fahintar junan a tsakanin yan ta'addan ya kara sanya su cikin al-amura na fasadi da sabo. Wani komandan yan ta'addan mai suna Abu Mohammad ya bayyana cewa dakarun da ake kira "rundunar yentaccen kasar Syria" mutane , barayi, yan fashi da kuma makasa.
Abu Mohammad ya kara da cewa, ya ga ayyukan ta'addanci da kisan mutanen da basu san hawa ko sauka ba wadan da wadan nan dakaru suka aikata. Ya kuma kara da cewa wani lokaci kwamandojinsu sukan umurcesu da kashe mutanen da basu san hawa ko sauka ba, a yayin su kuma suke kwasar dukiyoyin mutane.
A wani labarin kuma dangane da rikicin kasar ta Syria, gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad ta bada sanarwan cewa tana shirin gudanar da taron tattaunawa ta kasa da dukkan bangarori yan adawar kasar. Gwamnatin ta kara jaddada cewa ta yi imani cewa babu wata hanyar fita daga cikin rikicin da kasar ta Fada ciki in banda ta diblomasia da kuma tattaunawa.
1189429
captcha