IQNA

Nasrullah zai gabatar da jawabi danagne da abubuwan da ke faruwa a yankin musamman kan Syria

17:04 - February 16, 2013
Lambar Labari: 2497357
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar hizbullah a Lebanon zai gabbatar da jawabi kan muhimman abubuwan ad suke faruwa ayankin gabas ta tsakiya musamman a kasar Syria wadda makiya muslunci suka sako ta gaba da nufin rusa ta da kuma karya bangarorin da ke jagorancin gwagwarmaya a yankin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Almanar, cewa Sayyid Nasrullah babban sakataren kungiyar hizbullah a Lebanon zai gabbatar da jawabi kan muhimman abubuwan ad suke faruwa ayankin gabas ta tsakiya musamman a kasar Syria wadda makiya muslunci suka sako ta gaba da nufin rusa ta da kuma karya bangarorin da ke jagorancin gwagwarmaya a yankin baki daya.
A wani bangare kuma rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami nasarar hallaka wasu jami'an sojin kasar Turkiyya su hudu da suke taimakawa 'yan ta'addan da suke yakar gwamnatin kasar Siriya a wani ba ta kashi da ya gudana tsakanin sojojin Siriya da 'yan ta'ddan a garin Halab.
Tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran ta jiyo wata majiyar sojin kasar Siriyan tana fadin cewa a gumurzun da ya gudana a jiya tsakanin sojojin Siriya da 'yan ta'adda masu dauke da makami a yankin Al-Bab, sojojin kasar Siriya sun sami nasarar hallaka sojojin Turkiyya su hudu da kuma wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan.
Majiyar sojojin Siriya ta kara da cewa sojojin sun kai wannan harin ne bayan da suka sami labarin kasantuwar sojojin Turkiyyan a wajen don taimakawa 'yan tawayen, don haka suka kai harin da nufin kama su, sai dai kuma ba su sami damar kama ko da guda daga cikinsu ba, sai dai wadanda suka hallaka din.
Cikin 'yan kwanakin nan dai 'yan ta'addan da suke samun goyon bayan kasashen Turkiyya, Qatar da Saudiyya, sun kara irin hare-haren da suke kai wa cibiyoyin gwamnati da na soji a garin na Halab da nufin kwato su.

1189233

captcha