Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana rasuwar babban malamin addinin muslunci khoshvat da cewa babban rashi ne ga dukkanin musulmi tare da bayyana shi a matsayin abin koyi a cikin dukaknin ayyukansa na yada ilimin da yi musulmi jagoranci bias sahihin tafarki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani sakon ta’aziyya da ya tura a yau jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana rasuwar babban malamin addinin muslunci khoshvat da cewa babban rashi ne ga dukkanin musulmi tare da bayyana shi a matsayin abin koyi a cikin dukaknin ayyukansa na yada ilimin da yi musulmi jagoranci bias sahihin tafarki da kuma sadaukantarwa.
A wani bangaren kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun-dubatan mutanen garin Tabriz don tunawa da yunkurin 29 ga watan Bahman na mutanen Tabriz a shekarar 1356. A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin wannan ganawar, Jagoran ya yi karin haske kan maganganun jami'an gwamnatin Amurka dangane da batun tattaunawa da Iran da kuma shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar, kamar yadda kuma ya sake jinjinawa al'ummar kasar Iran sakamakon fitowar da suka yi ranar 22 ga watan Bahman don tunawa da ranar da juyin juya halin Musulunci na kasar ya yi nasara da kuma batun rikicin da ya faru a majalisar shawarar Musulunci ta kasar.
1192314