IQNA

An zargi mahukuntan kasar Faransa da takurawa mabiya tafarkin addinin muslunci

18:26 - February 20, 2013
Lambar Labari: 2500065
Bangaren kasa da kasa, an zargi mauhukuntan faransa da daukar matakai na takura mabiya addinin muslunci a kasar musamman mata daga cikinsu da suke saka hijabin muslunci wanda wasu daga cikin mahukuntan kasar da suke da ra’ayin kiyayya da musulunci suke sukar hakan matuka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wasu masana sun zargi mauhukuntan faransa da daukar matakai na takura mabiya addinin muslunci a kasar musamman mata daga cikinsu da suke saka hijabin muslunci wanda wasu daga cikin mahukuntan kasar da suke da ra’ayin kiyayya da musulunci suke sukar hakan matuka a bayyane a cikin kasar.
A bangare guda kuma hare haren da sojojin kasar Faransa suke kai wa kan 'yan tawayen Mali da suke mamaye da yankunan arewacin kasar, a farkon lamari hakan ya faranta ran jami'an gwamnatin kasar ta Faransa, amma a halin yanzu akwai rahoton cewa jami'an gwamnatin Faransa sun fara shiga cikin halin fargaba kan yiyuwar fuskantar hare haren daukan fansa daga 'yan kungiyar da sauran kungiyoyin da suke mara musu baya da suke cikin kasar ta Faransa.
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bada umurnin tsaurara matakan tsaro a muhimman wajajen taruwan jama'a a duk fadin kasar a matsayin riga kafin yiyuwar kai harin daukan fansa dangane da hare haren da sojojin Faransa ke kai wa kan 'yan tawayen kasar Mali. Hakika wannan mataki da shugaban kasar Faransa ya dauka na bada umurnin tsaurara matakan tsaro a matsayin riga kafi lamari da ya zo bayan fuskantar barazana daga kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addinin Islama.
Kakakin kungiyar Al-Qa'ida a yankin arewacin Afirika Abdullahi Asshinaqidi ya gargadi gwamnatin Faransa kan ta janye aniyarta na shiga cikin tawagar rundunonin sojin da za a aike zuwa kasar Mali domin yakar 'yan tawayen kasar, kuma ta hanzarta janye sojojinta da suke cikin kasar ta Mali. Har ila yau shugaban kungiyar Tauhid waj-Jihad a nahiyar yammacin Afirika.
1192361


captcha