IQNA

An tuhumci 'yan kungiyar Salafiya Da Hannu Wajen Kashe jagoran adawa na kasar Tunisia

10:45 - February 27, 2013
Lambar Labari: 2503214
Bangaren kasa da kasa, an zargi magoya bayan kungiyar salafiyya masu kafirta al'ummar musulmi na kasar Tunisia da hannu wajen kasha jagoran adawa na kasar Tunisia Shukri Balid domin haddasa rikici tsakanin al'ummar kasar kasantuwar cewa yana da matsaya da ta yi hannun riga da ta su.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da Gidan Talbijin na Almayadin na Kasar Labanan ya Habarto a yau Litinin, magoya bayan Jam’iyar Alnahda suka cinnawa Tutar Kasar Faransa wuta a Garin Suse inda suka yi Allawadai da Kasar Faransa. Shugaban Jam’iyar Rashid Ganushi yace:Kasar Faransa tafi ko wace Kasa kiyaya da Musulinci cikin Kasashen yammacin Turai. A nashi bangaren Ministan tsaron Kasar Faransa Claude Gyan ya maida martani, inda ya zargi Jam’iyar Alnahda da sanya shera’al Islama a Salon Milkin Kasar Tunisiya.

Abin tini a nan shine tun bayan samun nasarar Jam’iyar Alnahda a Kasar tunisia, Kasar Faransa bata amince da nasarar sai bayan kwana biyu. A lokacin shugabancin tsohon shugaban kasar ta Tunisia Zainul Abidin gwamnatin Kasar Faransa ta haramta wa Rashid Alganushi shiga cikin Kasar ta Faransa.

Kasar Tunisai ta fada cikin wani sabon rikicin siyasa ne bayan kisan da wasu yan bindiga wadanda har yanzu ba'a tantance ko suwaye ne ba suka yiwa wani fitaccen dan siyasar kasar kana kuma kuma madugun yan Adawa Chokri Belaid . Kisan wannan dan siyasar dai ya kara jefa kasar cikin wani sabon rikicin siyasa, in da yan adawa suka soma zanga-zanga da kuma yaje-yaje aiki na gama-gari, suna zargin gwamnatin jam'iyyyar masu kishin addinin ta Ennahdi da kashe shi.

Yana daga cikin abubuwan da suka biyu bayan kissan Chokri Belaid, gamayyar jam'iyyun adawa wadanda ba ruwanmu da addini su ka bayyana cewa za su fice daga kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin kasar, har'ila yau suka yi kira ga magoya bayan su da su shiga yajin aikin gama-gari, don nuna fushinsu da kisan mutumin nasu. A kokarin da gwamnatin kasar ta yi na kwantar da hankalin yan adawar Firayim Ministan kasar ta Tunisia, Hamadi Jebali, ya bayana cewa zai kafa gwamnatin kwararru , wacce ba ta da alaka da 'yan siyasa, wacce kuma za ta tafiyar da al'amurran kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben kasa baki daya nan gaba. Amma shawarar tasa bata sami amincewar jam'iyyar sa ta yan uwa musulmi ba.

Daga karshe dai Prrimista Jebali ya bayyana saukarsa daga mukamin Priminista a ranar tarlatan da ta gabata don bada damar zaben sabon Primista wanda zai yi kokarin kafa sabuwar gwamnati kamar yadda jam'iyyyar Ennada take so. Priministan ya dau wannan matakin ne bayan ganawarsa da shugaban kasar ta Tunisia Moncef Marzouki , ya kuma kara da cewa ba zai shiga takarar zabe mai zuwa ba. Sai bayan murabus din da ya yi jam'iyyar Ennahdi ta sake gabatar da sunan Jebali a matsayin wanda suke son ya jagoranci gwamnatin kasar, samma ya nemi uzurinsu, ya kuma ki karban matsayin.

1195513



























captcha