IQNA

Gwamnatin Faransa ta musanta cewa zata janye sojojinta daga Mali a wata mai kamawa

10:44 - February 27, 2013
Lambar Labari: 2503216
Bangaren kasa da kasa, ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a jiya Talata ya bayyana cewa; Maganar janye sojojin kasar Faransa daga cikin kasar Mali a nan kusa kadan, batu ne da bai dace ya taso ba a halin yanzu saboda sojojin na Faransa suna fuskantar yaki mai sarkakiya a tsaunukan da suke yankunan arewacin kasar ta Mali.
Jean-Yves Le Drian ya kara da cewa: A halin yanzu haka sojojin Faransa suna tsakiyar fafatawa ne da mayakan 'yan tawayen Mali musamman a yankunan tsaunukan Adrar des Ifoghas; har ila yau ministan tsaron kasar ta Faransa ya yi furuci da cewa; Yakin da kasar Faransa ke jagoranta a kasar Mali a halin yanzu ya lashe tsaban kudade da suka kai kimanin dalar Amurka miliyan dari da talatin da uku.
Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin bom da aka kai a garin Kidal da ke arewacin kasar Mali,Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa: Wata mota da aka makare da bama bamai ta tarwatse a wani wajen binciken ababan- hawa a garin Kidal da ke arewacin kasar Mali, inda harin ya yi sanadiyyar lashe rayukan mutane akalla hudu a jiya Talata.
Garin Kidal dai yana daga cikin manyan garuruwan da sojojin Faransa da na Mali suka kwace daga hannun 'yan tawayen kasar masu tsaurin ra'ayin addinin Islama, tun bayan da sojojin Faransa suka fara kai hare- hare ta sama da kasa kan yankunan da suke arewacin Mali a ranar 11 ga watan Janairun wannan shekara.

1195178




captcha