IQNA

Sayyid Nasrullah ya gargadi Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan tunanin wani shishi a Lebanon

23:19 - March 01, 2013
Lambar Labari: 2504149
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da cewar zata fuskanci dubban makamai masu linzami a kan birnin Tel Aviv da sauran garuruwan yahudawan sahayoniyya matukar ta yi gigin kaddamar da hari kan kasar Labanon. A jawabinsa a taron juyayin a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon a yau Lahadi.

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar tabbas gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana sane da irin bala'in da zai sauka a kanta matukar ta yi gigin daukan matakin kaddamar da harin wuce gona da iri kan kasar Labanon. Nasrullahi ya kara da cewar makamai masu linzami kirar Fajar-5 da 'yan gwagwarmayar Palasdinawa suka yi amfani da su, sun girgiza haramtacciyar kasar Isra'ila, to ina kuma dubban makamai masu linzami da kungiyar Hizbullahi zata harba kan kowane sako na haramtacciyar kasar ta Isra'ila musamman kan birnin Tel Aviv?. Har ila yau babban sakataren kungiyar ta Hizbullahi ya bayyana gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin makiyar al'ummar musulmin duniya, kuma duk wani mai jin cewa shi abokin haramtacciyar kasar Isra'ila ce, to shakka babu bawa ne ga yahudawan sahayoniyya.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, babu banbancin manufa a tsakanin dukkanin bangarorin siyasar haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummomin larabawa da musulmi. Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a wani jawabi dazun nan a birnin Beirut a taron maulidin manzon Allah, wanda aka nuna kai tsaye a allunan talabijin, ya ce yadda zaben ya gudana a haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin makon nan ya tabbatar da cewa akwai babbar matsalar siyasa a tsakanin manyan jami'an haramtacciyar kasar, amma kuma a lokaci guda hakan ba ya nufin cewa akwai banbanci a tsakaninsu kan yadda suke kallon musulmi da larabawa a matsayin manyan makiyansu.

Sayyid nasrullah ya jadda cewa babban abin da ke gaban musulmi shi ne fahimtar hakikanin koyarwar manzon Allah da kuma yin aiki da wannan koyarwar a cikin dukkanin bangarorin rayuwarsu, domin kuwa wannan shi ne hakikanin addinin muslunci wanda makiyansa ke hankoron ruwa, ta hanyar cin zarafin wannan manzo mai madaukakin matsayi da daraja, kamar dai yadda duniya take shedawa a halin yanzu.

1195975































captcha