Bangaren kasa da kasa, Limamin da ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran na kasar Iran ya jaddada cewa; Al'ummar Iran ba zasu taba amincewa da duk wata shawarar dakatar da shirin makamashin nukiliyar kasar na zaman lafiya ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, A hudubar sallar juma'arsa ta yau a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hujjatul-Islam Kazim Siddiqi ya bayyana cewa: Mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya hakkin al'ummar Iran ne, don haka babu wani karfi a duniya da zai tilasta musu janyewa daga kan hakkinsu.
Kazim Siddiqi ya kuma jaddada cewa: Al'ummar Iran ba zasu taba amincewa da duk wata shawarar dakatar da shirin makamashin nukiliyar kasar na zaman lafiya ba, kuma babu wani jami'in Iran da ke da hakkin daukan matakin dakatar da shirin.
Har ila yau Hujjatul-Islam Siddiqi ya fayyace cewar al'ummar Iran sun shafe tsawon shekaru 34 suna kalubalantar manyan kasashen duniya masu girman kai, kuma sun samu gagarumar nasara kan duk wani makircin da makiya ke kitsawa kan kasarsu.
1196792