Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar al-misry ta nakalto mataimakin shugaban kasar Imad Abdulgafur yana cewa; Da dama daga cikin manyan kasashen duniya ba su son ganin an sami zaman lafiya da lumana ko ci gaban tattalin arziki a kasar Masar, saboda sun yi kwanton bauna suna haddasa rikici.
Mataimakin shugaban kasar ta Masar ya ci gaba da cewa: Masar a halin yanzu tana fama da matsalar gudana da sha'anin mulki abinda ya zama wajibi a sake farfado da shi domin kasar ta sami ci gaba." Abdulgaffar dai yana gabatar da jawabi ne a bikin kafa cibiyar jam'iyyarsa ta al-watan a garin Suese, ya kuma kara da cewa; Adawar kasashen wajen ga Masar ta samo asali ne daga kokarin da Masar din ta ke yi na gina mashigar ruwan Sues.
Tun bayan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya isa birnin Alkahira na kasar Masar a jiya, dubban mutane a birane daban-daban na kasar ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da ziyarar tasa.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam raotanni daga birnin Alkahira ya habarta cewa, a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka ya isa birnin Alkahira, masu zanga-zanga sun cika titunan da ke isa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin, inda suke ta rera take mutuwa ga Amurka, yayin da wasu kuma suke rera taken Allawadai da shugaba Myhammad Mursi, wanda suke zarginsa da cin amanar kasa tare da zama dan amshin shatan Amurka.
A garin Port Said kuwa, daruruwan masu zanga-zanga ne suka kai farmaki kan hedikwatar 'yan sanda da ke birnin, inda suka cinna mata wuta, kuma suka hana 'yan kawana-kwana isa wurin, har sai da hedikwatar 'yan sandan ta kone kurmus.
1197983