IQNA

Mahukunta a kasar Bahrain na ci gaba da yin watsi da duk wani batun tatatunawa da 'yan adawa

20:08 - March 03, 2013
Lambar Labari: 2505472
Bangaren kasa da kasa, mutum guda ya rasa ransa kana wasu da dama sun sami raunuka a kasar Bahrain sakamakon diran mikiyan da jami'an tsaron kasar suka yi wa masu zanga-zangar neman 'yanci a kasar wadanda suka fito kan titunan babban birnin kasar, Manama, don tunawa da shekaru biyu da kaddamar da juyin juya halin neman sauyi a kasar.

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Bahrain din sun ce sakamakon bude wutan da jami'an tsaron kasar suka yi wa masu zanga-zangar a yau din nan Alhamis hakan ya yi sanadiyyar shahadar wani yaro dan shekaru 16 a duniya mai suna Husain Ali Ahmad Al-Jaziri da kuma raunana wani adadi mai yawa na masu zanga-zangar.
Har ila yau rahotannin sun ce har ya zuwa yanzu ana ci gaba da ba ta kashi tsakanin masu zanga-zangar wadanda suka sha alwashin ci gaba da zama a kan titunan kasar da kuma jami'an tsaron wadanda suke samun goyon bayan sojojin kasar Saudiyya.
A ranar 14 ga watan Fabrairun shekara ta 2011 ne dai al'ummar kasar Bahrain din suka kaddamar da juyin juya halinsu na ganin bayan 'ya'yan gidan sarautar Al-Khalifa da suka jima suna zaluntarsu sannan kuma suka ci gaba da wannan yunkuri na su duk kuwa da halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa suka nuna wa irin zaluncin da ake yi musu.
Na’ibin limamin juma’ar na Tehran yayi ishara da irin goyon baya ido rufe da Amurka take ba wa HKI wajen take hakkokin al’ummar Palastinu da take yi da kuma irin taimako da goyon bayan da take ba wa kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya a matsayin wasu daga cikin misalan da suke tabbatar da take hakkokin bil’adama da kuma goyon bayan aikin ta’addanci da Amurkan take yi inda ya ce: A halin yanzu Amurka tana shirin ba wa ‘yan ta’addan kasar Siriya makamai masu guba don su aikata laifin yaki da kuma kisan kiyashi a kasar Siriyan.
Ayatullah Khatami ya ce: Amurka ta rufe ido kan irin danyen aikin da azzaluman sarakunan Bahrain suke yi a kan al’ummar kasar inda take ci gaba da kwadaitar da su da kuma goya musu baya wajen ci gaba da take hakkokin al’ummar Bahrain.
Har ila yau Ayatullah Khatami ya jinjinawa nasarar da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran suka samu wajen sauko da jirgin sama mara matuki na leken asirin Amurka a kwanakin baya kamar yadda kuma ya kirayi al’ummar kasar da su kara hakuri da kuma tsayin daka wajen fuskantar matsin lamba na tattalin arziki da ake musu yana mai cewa daga karshe dai al’ummar Iran za su nasara kan makiyansu.
1198121






captcha