IQNA

Ci gaba da kisan gilla kan mabiya mazhabar shi’a a Pakistan na kara tsananta

20:40 - March 04, 2013
Lambar Labari: 2506129
Bnagaren kasa da kasa, kisan gillan da kungiyoyin yann ta’adda key i kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Pakistan yana ta kara tsananta a lokacin da kasashen da suke daukar nauyin wannan ta’addanci suke yin gum da bakunansu, musamman wadanda ake zargi daga cikinsu kamar saudiyya da kuma Qatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, mabiya mazhabar shi'a a birnin Quetta na kasar Pakistan ya sun bukaci majalisar dokokin kasar Paksitan ta yi zama ta musamman don tattauna kan hare haren da ake kaiwa al-ummar shi a yankin Bulucistan na kasar. Abdul Khaliq Hazara shugaban jam'iyyar Hazarat Democratic Party HDP ne ya yi wannan kira a jiya asabar kuma ya ce yakamata Primistan Raja Pervez Ashraf ya kira jami'an yansandan ciki na kasar su gabatar da bayanan irin hare haren ta'addanci da ake kaiwa mabiya mazhabar shia a birnin Quetter n akasar.
A ranar 16 –Febreru da muke ciki ne aka kai wani harin kunan bakin wake a kan mabiya mazhabar shia ta Hazara shia a birnin Queter wanda ya lashe rayukan yan shia 90 sannan ya raunata wasu 200. Har'ila yau kafin haka a ranar 10 –ga watan wani harin ya kashe yan shia shima fiye da 90. A ranar jumma'a da ta gabata ce jami'an tsaro a kasar Pakistan suka kama Malik Ishaq shugaban kungiyar yan ta'adda ta Lashkar-e-Jhangvi wacce take daukar nauyin kai irin wadannan nhare hare wanda ke zaune a garin Rahim Yar Khan.
1198640

captcha