IQNA

Mutanen kasar India na fuskantar matsaloli da dama ta fuskar rayuwa

20:42 - March 04, 2013
Lambar Labari: 2506130
Bangaren kasa da kasa, Lalacewar cibiyoyin bada wautan lantarki a kasar India a jefa fiye da rabin mutanen kasar biliyon cikin duhu a yau talata. Yankewar wutan lantarkin ya rutsa da masu hakar ma’adianai a karkashin kasa, ya dakatar da zirga zirgan jiragen kasa da kuma jefa asbitoci da dama cikin duhu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wannan dais hi ne lalacewar cibiyoyin bada wutan lantarki mafi muna wanda kasar ta fuskanta a fiye da shekaru guma da suka gabata. Katsewar wutan yan fara daga yankin Assam kusa da kasar China har zuwa yankin himalayar da kuma saharar Rajasthan . Shugaban kamfanin bada wutan lantarkin kasar ta India Nayak, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa kafin ma su gano dalilin da suka jawo katsewar wutan a jiya litinin sai suka kara samun yankewar wutar a wasu Karin yankunan a yau talata.
Ministan makamashin kasar ta India Sushilkumar Shinde, ya dora laifin katsewar wutan kan jihohin da suke zukar wutan fiye da yadda aka kayyada masu, wanda hakan ya jawo rikicewar tsarin rabon wutan. Fiye da mutane miliyon a jihohi fiye da 12 ne katsewar wutan ya jafasu cikin duhu. Masu hakar ma’adinin Coal kimani dari biyu ne aka rutsa da su a cikin rami a yammacin jihar Bengal a lokacinda injin lifata da ke jigilarsu ta tsaya cik.
Wasu jami’an kamfanin hakar coal a gabacin kasar sun bayyana cewa masu hakar ma’adinai wadanda suke kimanin mita dari bakwai a karkashin kasa a yankin dai basu shiga wani hatsari sanadiyyar rashin wutar ba. Jaragen kasa a garin kalata duk sun tsaida ayyukansu.
1198672
captcha