Bangaren kasa da kasa, hare haren wuce gona da irin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankunan Palasdinawa a cikin watanni shida da suka gabata sun yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa akalla sittin da bakwai.
Cibiyar kare hakkin bil-Adama ta Attadhamun a rahoton da ta fitar a jiya laraba ta bayyana cewar hare haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin Zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan daga farkon wannan shekara ta 2012 zuwa watan Yunin da ya gabata; akalla Palasdinawa 67 ne suka shahada, kuma 16 daga cikinsu kananan yara ne gami da mata 4. Cibiyar ta Attadhamun ta yi Allah wadai da ayyukan ta'addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da bayyana gwamnatin a matsayin mai nuna wariya ga Palasdinawa da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait (KUNA) ya bayyana cewar sakamakon kin amincewa da fitar da wani bayani kan shahadar wannan Palastinen da kwamitin tsaron ya yi biyo bayan gabatar da bukatar hakan da kasar Morocco ta yi, jakadar kasar Pakistan a MDD a madadin sauran kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ya bukaci kwamitin tsaron da ya sauke nauyin da ke wuyansa dangane da fursunoni Palastinawa da suke cikin mawuyacin hali a gidajen yarin HKI.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, jakadan kasar Pakistan din a MDD Mas'ud Khan ya ce Palastinawan da suke ci gaba da yajin cin abinci a gidajen yarin HKI suna cikin mawuyacin hali, wanda gudanar da bincike kan wannan lamari wani nauyi ne da ke wuyan kwamitin tsaron.
1199603