IQNA

Zaman tattaunawar addinai tsakanin mabiya addinin muslunci da fadar Vatican

22:39 - March 05, 2013
Lambar Labari: 2506859
Bangaren kasa da kasa, manyan fada-fada na maja'mi'ar Roman Katolika sun fara isa fadar Vatican a matsayin share fagen zabar sabon paparoma. Shugaban majalisar koli ta malaman addinin masu matsayin cardinal-cardinal, Angilo Dudano, ya gayyaci masu wannan matsayin na Cardinal da kuma Bishop su 209 da su halllara a fadar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daga gobe litinin ne dai za bude taron na malaman addini a cikin fadar ta Vatican domin tattauna matsalolin da majami'ar ta ke fuskanta. Masu matsayin Cardinal 66 da su ke a wajen kasar Italiya sun isa Vatican ko kuma suna kan hanya, yayin da sauran masu mukamin na Cardinal 75 su ke cikin kasar ta Italiya. Sai dai har yanzu ba a tantance ranar da za bude zaben na sabon Paparoma ba.

A wani rahoton kuma gwamnatin Iran ta ce ba ta bukatar gudanar da wata tattaunawa ta kai tsaye tare da Amurka, domin kuwa har inda yau take ba ta canja salon siyasarta ta gaba da hamhuriyar musulunci ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehmanparast ne ya bayyana hakan a yau, a lokacin da yake karba tambayoyin manema labarai a nan birnin Tehran, inda ya sheda cewa irin tsananin gabar da Amurka take nuna wa al'ummar kasar Iran, da kuma yadda take son ta nuna ita mai son sulhu ce tsakaninta da Iran, wannan lamurra ne biyu masu karo da juna, wadanda ba za su kasance a lokaci guda ba.

Mehmanparsat ya kara da cewa, babban abin da zai iya bayar da damar yin nazari kana bin da Amurka gabatar na neman tattaunawa da Iran shi ne, Amurka ta canja salon siyasarta ta gaba da Iran, kuma Iran din tag a hakan a aikace daga Amurka, kuma ta daina yin shigar shigula cikin harkokin kasashen yankin gabas ta tsakiya, to hakan zai iya bayar da damar yin nazari kan abin da ta gabatar.






1199138
captcha