Bangaren kasa da kasa, bababn malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya ce dole ne a gudanar da kuriar jin ra'ayin jama'a kan sakamakon tatatunawa tsakanin mahukunta da kuma bangarorin siyasar kasar domin al'umma su bayyana ra'ayinsu na amince ko rashin amincewa da hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin hudubar juma'a bababn malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya ce dole ne a gudanar da kuriar jin ra'ayin jama'a kan sakamakon tatatunawa tsakanin mahukunta da kuma bangarorin siyasar kasar domin al'umma su bayyana ra'ayinsu na amince ko rashin amincewa da hakan domin kada hakkinsu ya saraya.
Al’ummar kasar Bahrain na ci gaba da gudanar da Zanga-zangar neman kawo sauyin siyasa a kasarsu. Tashar telbijin din Press tv ta nun hotunan masu Zanga-zanga a jiya laraba a cikin birane da garuruwa mabanbanta na kasar suna masu yin Allah wadai da siyasar danniya ta zuri’ar ali-Khalida.
Masu Zanga-zangar sun kuma bukaci mahukuntan kasar da su mika gawar daya daga cikin wadanda jami’an tsaro su ka kashe a baya. A ranar talatar da ta gabata ma an yi Zanga-zangar yin Allah wadani da yadda mahukuntan kasar ke ci gaba da rike gawar Mahmud al-Jaza’iry, wanda jami’an tsaro su ka harbe.
Shekaru biyu kenan a jere da al’ummar Bahrain su ke gudanar da gangami da kuma Zanga-zangar lumana da ruwan sanyi domin neman kawo sauyin siyasa a cikin kasar. Sai dai mahukuntan kasar wadanda sojojin Saudiyya su ke rufawa bayan suna amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar ta lumana.
1201033