IQNA

Mahukuntan Bahrain Sun Tsananta Farmakinsu Kan fararen Hula A lokacin Tuanawa Da Mamayar Saudiyya

16:51 - March 15, 2013
Lambar Labari: 2511394
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun dauki matakai dab a a saba ganin irinsu ban a kai munan farmaki da mggan makamai kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar a daidai lokacin da ake tunawa zagayowar shekaru biyu da Saudiyya ta fara mamamya a kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, sarakunan kasar Bahrain sun dauki matakai dab a a saba ganin irinsu ban a kai munan farmaki da mggan makamai kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar a daidai lokacin da ake tunawa zagayowar lokacin da sojojin Saudiyya suka kaffamar hari da mamamaya kan al'ummar Bahrain.

A bangare guda kuma majiyar ma'aikatar harkokin wajen Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin tallafawa ayyukan ta'addanci a kasashen Bahrain da Yeme wanda ministocin harkokin cikin gida na kasashen larabawa suka yi mata a taron da suke gudanarwa a birnin Riyad na kasar Saudia a jiya Alhamis. Majiyar ta kara da cewa, abin mamaki da wannan zargin shi ne yadda wadan nan ministoci suka runtsa idanunsu kan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasar Syria kusan ko wace ranar Al.. wadanda kuma gwamnatocin wasu kasashen duniya suka fito fili suka bayyana cewa suna da hannu cikinsa.

Banda wannan kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama, ta kasa da kasa sun tabbatar da cewa yan ta'adda masu samun tallafi daga kasashen wajen sun aikata ayyukan ta'addanci a cikin yakin da suka soma da gwamnatin shugaba Asad na kasar Syria tun cikin watan Maris na shekarata 2011. A jiya Alhamis ne ake cika shekaru biyu da mamayar da sojojin kasar Saudia suka yiwa kamar Bahrain a kokarin da suke yi na murkushe zanga zangar lumanan da mutanen kasar suke ci gaba da yi don neman hakkinsu na zaben shugaban da zai jagorance su a kasarsu. Majiyar ma'aikatan harkokin wajen kasar Iran ta kara jadda cewa zargin na kungiyar kasashen larabawa bai da tushe ballantana makama.

1204532





















captcha