IQNA

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar la'anatar sojojin wahabiyawa 'yan mamaya a Bahrain

16:51 - March 15, 2013
Lambar Labari: 2511397
Bnagaren kasa da kasa, al'ummar kasar Bahrain an ci gaba da gudanar da jerin gwanoa dukkanin fadin kasar domin la'antar sojojin wahabiyawa masu mamayar kasar Bharain tun kimanin shekaru biyu da suka gabata tare da amincewar kasashen larabawan yankin da ke amshin shata ga mahukuntan Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga jiya har zuwa yau al'ummar kasar Bahrain an ci gaba da gudanar da jerin gwanoa dukkanin fadin kasar domin la'antar sojojin wahabiyawa masu mamayar kasar Bharain tun kimanin shekaru biyu da suka gabata tare da amincewar kasashen larabawan yankin da ke amshin shata ga mahukuntan kasashen yammacin turai.
A wani rahoton kuma ma'aikatar harkokin wajen Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin tallafawa ayyukan ta'addanci a kasashen Bahrain da Yeme wanda ministocin harkokin cikin gida na kasashen larabawa suka yi mata a taron da suke gudanarwa a birnin Riyad na kasar Saudia a jiya Alhamis. Majiyar ta kara da cewa, abin mamaki da wannan zargin shi ne yadda wadan nan ministoci suka runtsa idanunsu kan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasar Syria kusan ko wace rana wadanda kuma gwamnatocin wasu kasashen duniya suka fito fili suka bayyana cewa suna da hannu cikinsa.
Banda wannan kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama, ta kasa da kasa sun tabbatar da cewa yan ta'adda masu samun tallafi daga kasashen wajen sun aikata ayyukan ta'addanci a cikin yakin da suka soma da gwamnatin shugaba Asad na kasar Syria tun cikin watan Maris na shekarata dubu biyu das ha daya.
A jiya Alhamis ne ake cika shekaru biyu da mamayar da sojojin kasar Saudia suka yiwa kamar Bahrain a kokarin da suke yi na murkushe zanga zangar lumanan da mutanen kasar suke ci gaba da yi don neman hakkinsu na zaben shugaban da zai jagorance su a kasarsu.
1204011


captcha