Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya wasu daruruwan mata a palastinu sun yi zanga-zangar nuna kin amincewa da cin zarafin da yahudawan sahyuniya suke yi kan palstinawa da kuma abubuwa masu tsarki na addinin muslunci a cikin yankunansu musamman a masallacvin Qods da kuma yankunan gabar yda kogin Jordan.
A wani labarin kuma kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta duniya (NAM) ta bukaci kwamitin tsaron MDD da ta gudanar da bincike kan dalilan shahadar Arafat Jaradat daya daga cikin fursunoni Palastinawa da HKI take tsare da su wanda ya yi shahada a kwanakin baya.
Kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait ya bayyana cewar sakamakon kin amincewa da fitar da wani bayani kan shahadar wannan Palastinen da kwamitin tsaron ya yi biyo bayan gabatar da bukatar hakan da kasar Morocco ta yi, jakadar kasar Pakistan a MDD a madadin sauran kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ya bukaci kwamitin tsaron da ya sauke nauyin da ke wuyansa dangane da fursunoni Palastinawa da suke cikin mawuyacin hali a gidajen yarin HKI.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, jakadan kasar Pakistan din a MDD Mas'ud Khan ya ce Palastinawan da suke ci gaba da yajin cin abinci a gidajen yarin HKI suna cikin mawuyacin hali, wanda gudanar da bincike kan wannan lamari wani nauyi ne da ke wuyan kwamitin tsaron.
Kasashen Pakistan, Moroko, Togo, Rwanda da Jamhuriyar Azarbaijan suna daga cikin kasashe membobi wadanda ba na dindindin ba na kwamitin tsaron da suka sanya hannu kan wannan bukata.
1204816