Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana jin dadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da ci gaban da kasashen nahiyar Afrika ke samu a bangarori da dama.
A ganawar da ya yi da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza da tawagar da ke rufa masa baya a yau Laraba; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i ya tabo batun irin mummunan matakan da kasashen yammacin Turai da Amurka suka dauka kan kasashen nahiyar Afrika a lokacin da suka gudanar da mulkin mallaka kan kasashen nahiyar da kuma matakan da suke dauka a halin yanzu na kulla makirce-makirce da kunna wutan rikici a nahiyar,
Don haka jagoran juyin juya halin na Musulunci ya bayyana fatansa na ganin dukkanin kasashen nahiyar Afrika musamman kasar Burundi sun kai ga samun kyakkyawar makoma da ci gaba a dukkanin bangarorin rayuwa.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jaddada jin dadinsa kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Burundi tare da jaddada goyon bayan kasar Iran ga kungiyar tarayyar Afrika yana mai bayyana cewar kungiyar tarayyar Afrika zata iya zama wata cibiya mai karfi da zata dauki alhakin kare manufofin dukkanin kasashen nahiyar Afrika.
1211083