IQNA

Ana Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Harin Makaman Roka Da 'Yan ta'adda Suka A Yankin Kudancin Beirut

19:35 - May 27, 2013
Lambar Labari: 2539738
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyi da masana a cikin kasashen larabawa suna ci gaba da yin Allawadai da harin ta'addancin da wasu 'yan ta'adda suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon wanda mayakan kungiyar hizbullah suke cikinsa domin fushinsu kan jawabin Sayyid Nasrullah day a ce bas u bar Syria ta fada hannun Amurka da Isra'ila da masu cin naman mutane ne ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masana a cikin kasashen larabawa suna ci gaba da yin Allawadai da harin ta'addancin da wasu 'yan ta'adda suka kai kan yankin kudancin kasar Lebanon,a wani mataki na shigar da kasar cikin yakin da aka haddasa a cikin kasar Syria wanda Amurka da Isra'ila suke jagoranta.

Rahotanni daga kasar Syria sun habarta cewa dakarun gwamnatin kasar suna ci gaba da fatattakar 'yan bindiga a arewacin birnin Qusayr, a yunkurin da suke yi na tsarkake dukaknin yankunan kasar daga 'yan bindiga da ke samun goyon bayan Amurka da Isra'ila da wasu kasashe 'yan koransu.

Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga birnin na Alqusayr mai matukar muhimmanci ya bayyana cewa, a jiya Lahadi sojojin Syria sun kwace iko da yankin Hamidiyya, daya daga cikin manyan yankuna da ke arewacin birnin, bayan da suka kammala kwace iko da sauran yankunan gabaci da kudanci da kuma yammacin garin da 'yan bindiga ke iko da a lokutan baya. Dan rahoton na Alalam ya ce 'yan bindiga da dama sun mika kansu da makaman da ke hannunsu a jiya, yayin da aka kashe wani adadi mai yawa da suka ki mika kansu, daga cikinsu kuwa da kanar Osman Al-usair, wani babban jami'an sojin kasar Saudiyya, wanda yake jagorantar 'yan yawaye a Syria.

A bangare guda kuma gwamnatin kasar ta Syria ta bayyana aniyarta ta halartar taron birnin Janeva, da nufin samun hanyoyin kawo karshen rikicin, ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu'allim ya bayyana cewa, gwamnatin Syria ta bijiro da batun sulhu da warware wannan rikici tun daga lokacin da aka haddasa shi, amma 'yan adawa suka dage kan cewa sai sun kawar da gwamnati da karfin tuwu, kuma kasashen Amurka da wasu daga cikin turawa gami da Isra'ila suke ci gaba da taimaka musu kan hakan.



1234294


captcha