IQNA

Fatawoyin Qardawi Na Kiyayya Da Shi'a Sun Samo Asali Ne Daga Kiyayyarsa Da Ahlul Bait (AS)

21:34 - June 08, 2013
Lambar Labari: 2544125
Bangaren kasa da kasa, da dama daga cikin malaman addinin musluncmasu lamiri a duniya da suka hada da sunna da shi'a sun yi imanin cewa, rin kalaman batunci da malamin gwamnatin Qatar Yusuf Qardawi yake kan mazhabar iyalan gidan manzo, hakan ya samo asali ne daga kiyayyasa da ahlul bait.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, malaman Ahlussuna daga kasashen larabawa daban-daban na ci gaba da mayar da martani ga babban mai bai wa masarautar Qatar fatawa Yusuf Qardawi, wanda ya yi kira ga Ahlussuna na duniya da su tafi kasar Syria domin yaki da gwamnatin kasar.
Da dama daga cikin malaman Ahlussuna daga kasashen Jordan, Iraki, Palastine, Lebanon Masar sun mayar masa da martani da cewa, abin da ya fada fatawa ce daga aljihunsa, kuma ba ya da ikon ya yi magana da yawun ahlussuna na duniya baki daya domin aiwatar da manufofi na siyasar turawa ko wasu sarakunan larabawa, wanda kuma manufar hakan ita ce haifar da fitina tsakanin al'ummar musulmi na duniya baki daya, inda malaman suka ce da ya kamata ne ya bayar da fatawar yaki da yahudawan Isra'ila da suke kashe Palastinawa fiye da shekaru 60 da suka gabata, kuma suke ci gaba da mamaye masallacin Qods mai alfarma.
Qardawi ya bayar da fatawr tasa ne bisa hujjar cewa daruruwan mayakan kungiyar Hizbullah sun shiga yakin da ake yi a garin Qusayr da ke kan iyakan Syria da Lebanon, wanda kuma akasarin mazauna garin 'yan asalin kasar Lebanon, wadanda 'yan tawaye da ke samun goyon bayan Amurka da Isra'ila suka kore su suka mamaye garin tun shekaru biyu da suka gabata. Kungiyar Hizbullah ta sanar cewa ta shiga birnin Qusayr ne bayan tabbatar da cewa Isra'ila ce ke jagorantar yakin da ake yi a birnin, ba yaki ne na 'yan tawayen da sojojin kasar ba, Dalili na biyu kuma shi ne kare wuraren masu tsarki da ake rusawa a Syria, da suka hada da kabrukan sahabbai da na annabawa da na iyalan gidan manzon Allah, wanda hakkin dukkanin musulmi su ba su kariya.
1239219

captcha