IQNA

Zababben shugaban kasar Iran ya taya al'ummar kasar Murna kan nasarar zabe

18:03 - June 16, 2013
Lambar Labari: 2547996
Bangaren siyasa, zababben shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya mika godiya ga dukkanin al'ummar kasar, wadanda suka zabe shi da ma wadanda ba su zabe shi ba, tare da bayyana cewa dukkanin al'ummar Iran ne suka yi nasara a zaben da ya gudana lami lafiya a dukkanin fadin kasar.

Kamfainin dilalncin labaran Iqna ya ce, Dr. Rauhani ya mika godiya ta musamman ga jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, tare da sauran malaman addini da kuma masana daga bangarori daban-daban na kasar, inda su ne taka rawa matuka wajen sanya fata a cikin zukatan al'ummar kasar Iran, tare da karfafa gwiwarsu wajen nuna wa duniya cewa Iran kasa da al'umma suke da 'yanci wajen zabar makomarsu.

A bangare guda kuma Dr. Rauhani ya jinjina wa sauran 'yan takarar shugabancin kasa 5, tare da bayyana su a matsayin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen kara fito da matsayin Iran a demokradiyance bisa mahanga ta addini, tare da yin kira gare su da su dafa masa wajen yi wa al'ummar kasar Iran hidima.

Bayanin ya kara da cewa zababben shugaban kasar Iran Rauhani ya mika godiya ga dukkanin al'ummar kasar, wadanda suka zabe shi da ma wadanda ba su zabe shi ba, tare da bayyana cewa dukkanin al'ummar Iran ne suka yi nasara a zaben da ya gudana lami lafiya a dukkanin fadin kasar ta Iran baki daya.

1243622









captcha