IQNA

An tattauna kan matsalolin 'yan salafiyya da kuma yadda suke bata sunan musulunci

18:02 - June 22, 2013
Lambar Labari: 2550699
Bangaren kasa da kasa, manyan malaman addinin muslunci sun nuna damuwa matuka kan yadda mabiya tafarkin salafiyya suke bata sunan addinini musluncia idon duniya, wanda hakan ke bukatar daukar kwarar matakai.



Kafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya manyan malaman addinin muslunci sun nuna damuwa matuka kan yadda mabiya tafarkin salafiyya suke bata sunan addinini musluncia idon duniya, wanda hakan ke bukatar daukar kwarar matakai kan wannan matsala.

A bangare guda kumka A jiya laraba wata kafar tsaron Kasar Tunusiya ta bayyana cewa Dakarun Kasar na fafatawa da wata Kungiya ta ‘yan salafiya masu tsatsauren ra’ayi a anguwa kasrin dake yammacin birnin tunus . Ita dai wannan kungiya ta kumshe mutane 50 wanda wani dan Kasar Algeria tare da wasu ‘yan kasar Tunisiya biyu suka bada sanarwar jagorancinta.

Ya zuwa yanzu Jami’an Kasar Tunusiya ba su bayar da wata sanarwa ba kan wannan samamai da Dakarun Kasar suka kaiwa ‘yan kungiyar Salafiyar masu tsatsauren ra’ayi ba. Tun watan Decemba na shekarar da ta gabata Dakarun Kasar Tunisiya ke ta kokari don ganin sun rushe wannan kungiya. Ita dai wannan kungiya ta kafu ne bayan da wasu mayaka 11 wanda suka dauki alhakin wani hari da aka kai a Bou Chebka dake kan iyaka kasar da Kasar Algeriya wanda yayi sanadiyar kashe ma’aikaci guda daya.

A rahoton da kafar tsaron ta bayar na nuni da cewa wannan mayaka matasan anguwar Kasrin ne tare da mayakan da suka dawo daga kasar Mali.

1246256




captcha