IQNA

Kisan gilla kan mabiya tafarkin iayalan gidan Manzo a Masar sakamako ne na siyasar Morsi

17:53 - June 25, 2013
Lambar Labari: 2552096
Bangaren kasa da kasa, kisan gillar da ake yi wa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a cikin 'yan lokutanan nan sakamako ne na siyasar ta'asubanci ta Muhammad Morsi wanda yake kallon mabiya tafarkin shi'a amatsayin kafirai day a kamata azubar da jinisu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kisan gillar da ake yi wa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a cikin 'yan lokutanan nan sakamako ne na siyasar ta'asubanci ta Muhammad Morsi wanda yake kallon mabiya tafarkin shi'a amatsayin kafirai day a kamata azubar da jinisu kamar dai yadda malaminsa ya dora shi.

Ana ci gaba da fitar da bayanai na yin Allawadai da kisan gillar da wasu 'yan salafiya Takfiriyyah suka yi wa malami a jami'ar Azhar Shekh Hassan Shuhhat saboda bambancin Mazhaba, yayin da jami'ar ta Azhar ta bayyana hakan da cewa yana daga manyan zubbbai (kaba'ira) da aka aikata a tarihin kasar Masar. Shi kuwa madugun adawa na kasar Muhammad Barade'i ya ce wannan wani sabon abu ne mai matukar hadari da al'ummar kasar Masar suka fara gani sakamakon salon mulkin da ke tafiyar da kasar a halin yanzu.

Bangaren babban mai shigar da kara na kasar Masar Tal'at Ibrahim ya bayar da umurnin gudanar da binciken gaggawa kan wannan aiki da ya ce ya faru a gaban jami'an 'yan sanda, tare da kame duk wani wanda ake zargin yana da hannu cikin lamarin ba tare da wani bata lokaci ba kamar dai yadda ya fada.

1247702




captcha