IQNA

Mabiya tafarkin iyalan gidan amnzo a Masar za su bayyana matsayinsu kana bin da ke faruwa

17:54 - June 26, 2013
Lambar Labari: 2552719
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tababta a gare shi a kasar Masar za su bayyana matsayinsu dangane da abin day a faru na kisan babban malimin addinin muslunci a kasar bisa hujjar banbancin mazhaba.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar yaum sabi cewa, a yau mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tababta a gare shi a kasar Masar za su bayyana matsayinsu dangane da abin day a faru na kisan babban malimin addinin muslunci a kasar bisa hujjar banbancin mazhaba inda yake bin mazhabar Ahlul bait, wanda kuma suke da akidar kafirta musulmi suka kashe shi.

A jiya an gudanar da Jana’izar mabiyar tafarkin mazhabar Ahlulbait da ‘yan kungiyar Salifiya suka kashe a kasar Masar. A marecen yau talata ne a gudanar da zana’izar Mutane nan mabiya tafarkin mazhabar Ahlulbait guda 4 da ‘yan kungiyar salafiya suka kaisu da shahada. An bunne mutane 3 a masallacin Sayyidatun nafisa dake tsakiyar garin Alkahira wanda hakan ya kara kawo bacin ran al’umma ga kungiyar Salafiya a kasar sannan mutun guda an binne shine a garin Bahira dake arewacin kasar.
A ranar lahadi ne wasu ‘yan kungiyar salafiya suka kai hari a gidan Babban malamin nan Sheik Hasan Shuhata daya daga cikin shugabanin Shi’a a kasar Masar inda suka sameshi tare da dan uwansa da talibbansa guda biyu sannan suka kaisu da shahada.
Daga nata waje Gwamnati ta bada sanarwar kama Mutane 8 wadanda ake zarkin su kan cewa sunada hannu wajen kashe wadannan bayun Allah.
1248574





captcha