Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, A jawabin da ya gabatar a wajen wannan taron, Jagoran ya gode wa ma'aikatar shari'ar dangane da ayyukan da ta yi a lokacin zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuni. Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin fitowar da al'ummar Iran suka yi a lokacin zaben da kuma wajibcin taimakawa shugaban kasar da aka zaban, Jagoran cewa ya yi: Shan kashin dukkanin makirce-makircen da makiya suka kulla, bayyanar da yardar da mutane suke da ita ga gwamnatin Musulunci da kuma wadanda suka gudanar da wannan zaben, tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, girmama doka da ‘yan takaran zaben suka yi da kuma karfin da Jamhuriyar Musulunci take da shi wajen kare manufofinta suna daga cikin batutuwa masu muhimmanci da aka tabbatar da su a yayin wannan zaben.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin kulle-kullen da masu adawa da al'ummar Iran suka yi tsawon shekara guda don su yi tasiri cikin wannan zaben, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Makiya da masu adawa da Jamhuriyar Musulunci sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganin ba a gudanar da wannan zaben ba, ko kuma su kashe wa mutane gwiwa da hana su fitowa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Hatta bayan zaben ma sun tsara wasu makirce-makircen don su cimma bakaken aniyarsu ta hanyar fakewa da wasu abubuwa. To amma cikin yardar Allah, al'ummar Iran sun bayyana da irin girmar da suke da ita a ranar zaben. Don haka abin da ya faru sabanin abin da makiya suke fatan gani ne.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da kokarin da makiyan suka yi wajen yin sharhi maras tushe dangane da dalilan da suka sanya al'ummar Iran fitowa kwansu da kwarkwatansu lokacin zaben, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Sanya shakku dangane da ingancin zaben na daga cikin hanyoyin da makiya suka bi wajen kashe gwiwan mutane, to amma al'ummar Iran sun yi aikin da ya tilasta wa kafafen farfagandar ma'abota girman kai, a ranar zaben, yarda da kuma bayyanar da irin gagarumar fitowar da mutane suka yi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Babban dalilin fitowar al'umma yayin zaben bana, shi ne yarda da kuma kauna ta gaba daya da suke da ita ga tsarin Jamhuriyar Musulunci, yarda da masu sanya ido da kuma gudanar da zaben da kuma fatan da suke da shi na ci gaba da tafiya a kan tafarkin daukakar Iran.
Jagoran ya yi ishara da maganar da ya yi wasu ‘yan kwanaki kafin zaben shugaban kasar inda ya ce: A wancan lokaci na fadi cewa ko da a ce za a sami wasu mutane wadanda hankalinsu bai kwanta sosai da wannan tsarin ba, to amma sai ya zamanto suna kaunar ganin an kare manufofin kasar Iran, to su fito lokacin zaben. Don haka babu shakkar cewa akwai irin wadannan mutanen.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da ya faru ya tabbatar da cewa hatta mutanen da ba sa goyon bayan wannan tsarin, to amma sun yarda da tsarin zaben da ake gudanarwa din. Don kuwa sun san cewa Jamhuriyar Musulunci, ta tsaya kyam tamkar zaki, wajen fada da masu bakar aniya, sannan kuma da kyau tana ci gaba da kare manufofi da kuma daukakar kasar Iran.
Haka nan kuma a ci gaba da bayanin irin abubuwan da suka sanya wannan zabe ya yi fice, Jagoran ya yi ishara da irin yadda aka tabbatar da tsaro a lokacin wannan zaben wanda bayan zaben shugaban kasa har ila yau an gudanar da zaben majalisun kananan hukumomi a daidai lokacin.
Har ila yau kuma Jagoran ya yi ishara da irin girmama doka da sauran ‘yan takaran zaben na bana suka yi wanda yace shi ma lamari ne mai matukar muhimmancin gaske, kamar yadda kuma yayi ishara da irin yadda sauran ‘yan takaran suka taya zababben shugaban murnar nasarar da ya samu inda ya ce hakan ya kara irin farin cikin da mutane suke ciki.
Jagoran ya yi ishara da fitinar da wasu suka tayar bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2009 inda ya ce: A wannan zaben ma wasu suna iya fakewa da wasu abubuwa su haifar da fitina da rikici, to amma irin halin dattakon da sauran ‘yan takaran suka nuna, hakan ya kwantar da hankalun mutane da kuma faranta musu. Don haka wajibi ne a koda yaushe irin wannan girmama doka ta zamanto darasi ga kowa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin wannan fitowa da al'umma suka yi a lokacin zaben a matsayin wata falala da kuma taimako na Ubangiji da wajibi ne a gode wa hakan, kamar yadda kuma ya yi kiran da a taimaka wa zababben shugaban kasar wajen ciyar da kasar Iran gaba.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da batun shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar Iran da kuma ihu bayan harin da makiya suke ci gaba da yi kansa inda ya ce: Kamar yadda a farkon shekara na fadi, ‘yan wasu kasashe wadanda suke adawa da Iran sannan kuma suke kiran kansu da kasashen duniya su ne ba sa son a kawo karshen wannan batu na nukiliya. Idan da a ce sun yi watsi da irin wannan bakar aniya ta su, to da kuwa an magance wannan matsalar cikin sauki.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: A lokuta da dama an sha kai wa gacin magance wannan matsalar, to amma sai Amurkawa su shigo da wani sabon abin.
Jagoran yayi ishara da wata takarda da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta taba rubutawa da ke cewa babu wata matsala dangane da shirin nukiliyan na Iran, don haka an kawo karshen wannan lamari. To amma ba tare da bata lokaci ba sai Amurkawa suka sake gabatar da wani sabon abu. Don kuwa suna daukan batun nukiliya a matsayin wani makami na matsin lamba a kan Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da kokarin da sahyoniyawa suke yi a wannan bangaren inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi aiki da doka cikin wannan shiri na ta na nukiliya, to amma manufar makiyan ita ce ci gaba da matsin lamba, gajiyar da al'ummar Iran da kuma kokarin sauya gwamnatin Musulunci. A saboda haka ba za su taba bari a magance matsalar ba.
Jagoran ya ce batun nukiliya, hakkokin bil'adama da demokradiyya ba shi ne ya dami wadancan mutanen ba, babban abin da suka sa a gaba shi ne dakatar da irin ci gaban da Iran take samu da kuma sake tabbatar da ikonsu a kan al'ummar Iran. To amma Jamhuriyar Musulunci ta Iran da dukkan karfinta ta tsaya kyam kuma za ta ci gaba da tsayawa kyam wajen kare manufofin al'ummar Iran.
Jagoran ya ce tarihi dai ya tabbatar da cewa duk wanda ya yi tsayin daka a bisa tafarkin gaskiya to kuwa zai yi nasara. A saboda haka ko shakka babu al'ummar Iran za su nasara a kan makiyansu.
Tun da fari dai sai da alkalin alkalai sannan kuma shugaban ma'aikatar shari'a ta Iran Ayatullah Amoli Larijani ya gabatar da jawabinsa inda ya yi ishara da irin ayyukan da ma'aikatar tasa ta aikata tsawon shekara.
1248534