IQNA

Zanga-zanagar la'antar mahukuntan masar kan kisan malamin Shi'a a kasar

23:57 - June 27, 2013
Lambar Labari: 2552884
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zanga-zangar la'anatar mahukuntan kasar masar a gaban ofishin jakadancin kasar da ke birnin London na kasar Birtaniya dangane da kisan gillar da 'tan salafiyya suka yi bababn malamin addinin muslunci kuma malamin mabiya tafarkin ahlul bait.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daruruwan musulmi sun gudanar da zanga-zangar la'anatar mahukuntan kasar masar a gaban ofishin jakadancin kasar da ke birnin London na kasar Birtaniya dangane da kisan gillar da 'tan salafiyya suka yi bababn malamin addinin muslunci kuma malamin mabiya tafarkin ahlul bait (AS) sheikh Hassan Shehhata.
A bangare guda kuma wasu rahotanni sun ce wasu daga cikin almajiran Sheikh Hassan Shehhata dad a 'yan kungiyar salafiyya takfiriyyah na kasar Masar suka yi kisan gilla suka kira wani taron manema labarai a birnin Alkahira, inda suka bayyana matakan da za su dauka matukar dai mahukuntan kasar bas u kamo wadanda suka aikata wannan laifi ba.

Daga cikin almajiran Shehin marigayi Sheikh Hassan Shehhata da suka kira taron manema labaran a birnin Alkahira akwai lauyoyi da kuma malaman jami'a da likitoci da 'yan jarida, inda suka bai wa shugaban kasar ta Masar Muhammad Morsi wa'adin sa'o'i 48 da ya gano dukkanin wadanda suke da hannu wajen yi wa malamin kisan gilla, idan kuma ba haka ba, to za su shigar da kara a kotun manyan laifuka ta duniya a kan gwamnatin Masar.

A ranar lahadin da ta gabata ce dai wasu daga cikin mabiya akidar nan ta kafirta al'ummar musulmi da aka fi sani da salafiyya takfiriyyah, suka kai farmaki kan gidan Sheikh Hassan Shehhata, daya daga cikin manyan malamai a jami'ar Azahar, kumajagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar ta Masar, inda suka yi masa kisan tare da wasu almajiransu uku da ke wurin.

Wannan mummunan aiki dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga kungiyoyi na kasa da kasa, inda ajiya ma Kungiyar Amnesty International ta fitar da wani bayani, da a cikinsa ta kirayi mahukuntan kasar Masar da su gaggauta gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wa Sheikh Hassan Shehata da almajiransa uku, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin a gaban kuliya domin fuskantar hukunci, ba tare da bata lokaci ba.

1248287



captcha