Kamfain dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci an kasar Iraki Ayatollah Bashir najafi ya bayyana kisan babban malamin addinin muslunci da aka yi a kasar da cewa wannan aiki ne na shaidan da kuma masu neman haddasa fitina tsakanin al'ummar musulmi a duniyar yau.
Mataimakin limamin Juma’ar birnin Tehran ya yi kakkausar suka dangane da kisan gillan da ‘yan salafiyan kasar Masar suka yi wa Sheikh Hasan Shahata, daya daga cikin jagororin ‘yan Shi’an kasar Masar tare da almajiransa su uku yana mai bayyana hakan a matsayin wani lamari mai hatsarin gaske da ke fuskantar duniyar musulmi.
Hujjatul Islam Sheikh Muhammad Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a yau din nan inda ya ce ‘yan mulkin mallaka sun dauki shekara da shekaru suna kulla makircin kirkirar wannan kungiya ta ‘yan salafiya masu kafirta musulmi wadanda a halin yanzu suke ci gaba da zubar da jinin al’ummomi a duk fadin duniya don su bakanta sunan Musulunci. Don haka ya ja kunnen al’ummar musulmi da su yi taka tsantsan dangane da wannan makircin da ake ci gaba da yadawa da kudaden man fetur din wasu kasashen musulmi.
Yayin da ya koma kan zaben shugaban kasar Iran da aka gudanar da kuma kokarin da makiya suke ci gaba da yi na ba wa lamarin fassarori daban-daban, Sheikh Siddiqi cewa ya yi fitowar da al’ummar Iran suka yi a lokacin wannan zaben ta hana makiya cimma bakaken manufofinsu.
1250506