IQNA

Jami'ar Azahar ta kirayi dukkanin bangarorin siyasar kasar Masar ad su kawo karshen rikici

23:53 - July 03, 2013
Lambar Labari: 2556181
Bangaren kasa da kasa, Dangantakar dake tsakanin kasar Masar da Habasha dangane da gabar kogin Nile ta yi tsami saboda Habasha ta yi shirin kafa wata madatsar ruwa. Abin da ya kawo cece kuce mai tsanani a kasashen dake wannan yanki kan albarkatun ruwa. An ba da labari cewa, wannan madatsar ruwan da Habasha ta yi shirin gina wa yana kan kogin Blue Nile dake kan iyaka tsakanin Habasha da Sudan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta ewa, wadda ta kasance muhimmin mataki ne na kasar Habasha a cikin shekaru 25 masu zuwa wadda kuma ta shafi dala biliyan 12. Yawan wutar lantarki da za ta samar zai kai megawatt hakan ya sa za ta zama madatsar ruwa da za ta rika samar da wutar lantarki mafi girma a nahiyar Afrika. Amma wannan aiki zai kawo wasu kasashe dake matakin karshe na wannan kogi illa wajen yin amfani da albarkatun ruwa ciki hadda Masar. Wakilan kasashen Habasha, Masar, Sudan da kuma masanan kasa da kasa kan albarkatun ruwa sun taba kafa wani kwamitin kimantawa a watan Mayu na shekarar 2012 domin kimanta tasiri da madatsar ruwa za ta kawowa wadannan kasashen dake dab da kogin Nile.

A farkon watan Yuni na wannan shekara, bayan kwamitin ya gabatarwa Masar rahoton, rikicin dake tsakanin Masar da Habasha kan wannan batu ya kara tsananta. Ko da yake, gwamnatin Habasha ta sanar da cewa, wannan aiki ba zai rage yawan albarkatun ruwan da Masar za ta mallaka ba, amma a ganin Masar, Habasha ba ta gabatar da hakikanin bayani kan wannan aiki ba, idan ta kafa ita, yawan ruwan da Masar za ta samu daga kogin Nile zai ragu da kimanin cubic mita biliyan 10 a ko wace shekara, yawan wutar lantarki da madatsar ruwa za ta samar shi zai ragu da kashi 18 cikin dari. Ban da haka, jami'an gwamnatin kasar Masar sun dauki tsattsauran mataki kan wannan batu. Shugaban kasar Mohamed Morsi ya jaddada a gun wani taron da aka yi a ran 3 ga wata kan batun isashen ruwa na kogin Nile cewa, kasar za ta dauki matakai da suka dace domin ba da tabbaci ga isashen ruwa a kasar.

A ran 10 ga wanan wata ne, firaministan kasar Masar Hisham Qandil ya ba da sanarwa cewa, zai aiko ministan harkokin waje Mohamed Kamel Amr domin ya isa birnin Addis Ababa kan batun madatsar ruwa, tare kuma jaddada cewa, albarkatun ruwa na da alaka sosai da zaman rayuwar jama'ar kasar. Mai ba da shawara ga shugaban kasar, Ayman Ali, yayin da ya tabo wannan batu ya ce, ya kamata a kiyaye hakkin kasar na yin amfani da albarkatun ruwa. Ban da haka, shugaban jam'iyya dake kan matsayi na biyu a kasar, Younis Makhayoum ya ba da shawarar tura masu aikin leken asiri da su kai hari kan madatsar ruwa.

1251104







captcha