IQNA

Mabiya addinin musulunci na ciyar miskinai a kasar Faransa a cikin watan Ramadan

10:11 - July 13, 2013
Lambar Labari: 2559956
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin musulunci a kasar faransa suna ciyar da mabukata a lokacin buda baki a masallatai daban-daban na kasar Faransa a matsayin daya daga cikin kyawawan ayyuka da muslunci ya umurni da su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin mabiya addinin musulunci a kasar faransa suna ciyar da mabukata a lokacin buda baki a masallatai daban-daban na kasar Faransa a matsayin daya daga cikin kyawawan ayyuka da muslunci ya umurni da su kasantuwar muslunci a ddini ne na jin kai da kyautatawa ga dan adam.
Da dama daga cikin mabiya addinin muslunci a cikin kasashen turai sun fito ne daga kasashen larabawa da kuma Turkiya gami da kasashen nahiyar Afirka, karbar addinin muslunci da ake yi a cikin wadannan kasashe ya sanya gwamnatoci musamman ma irin su Faransa daukar matakan dakile yaduwar addini a cikin kasarta da ma sauran kasashen naiyar.
Rahoton ya ce mabiya addinin musulunci a kasar faransa suna ciyar da mabukata a lokacin buda baki a masallatai daban-daban na kasar Faransa a matsayin daya daga cikin kyawawan ayyuka da muslunci ya umurni da su domin jin kai.
1255992
captcha