IQNA

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya Gana Da Jami'ai

0:03 - July 22, 2013
Lambar Labari: 2564835
Bangarensiyasa, jagoran ya bayyana cewa Iran a shirye take ta yi mu'amala da sauran kasashen duniya amma bisa bisa girmama juna tare da bin dukaknin hanyoyi da aka sani na alaka tsakanin kasa da kasa, amma Iran ba za ta amince da cin zarafi ko baranaza ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne a 'yan sa'oin da suka gabata a lokacin buda baki tare da manyan jami'an gwamnatin kasar a nan birnin Tehran, ya ce Iran za ta yi mu'amala da sauran kasashe amma bisa girmama juna da kuma yin la'akari da daya bangaren yadda ya dauki wannan alaka.
Ya ce kasashen da suke da daddiyar gaba da Iran sharadin yin alaka da su shi ne ajiye gabarsu da makirkinsu a kan Iran, domin kuwa a cewarsa al'ummar kasar sun san masoyansu kuma sun san makiyansu na gaskiya.
Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya jinjina wa shugaban kasa mai barin gado Mahmud ahmadinejad, dangane da namijin kokarin da ya yi wajen gudanar da ayyuka na ci gaban kasar Iran a cikin shekaru 8 da ya yi yana shugabancin kasar. Jagoran ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake ganawa da shugaban mai barin gado tare da manyan jami'an gwamnatinsa, inda ya ce gwamnatin Ahmadinejad ta karfafa manufofi da dama na juyin juya hali a kasar, tare da yin aiki tukuri na ci gaban kasa da al'ummarta, wanda ya ce hakan shi ne abin fata ga kowace gwamnati da za ta zo nan gaba a kasar.

A nasa bangaren shugaban kasar Iran mai barin gado Mahmud Ahmadinejad, ya yi godiya ga jagoran kan goyon baya da kuma karfin gwiwa da ya bas hi domin gudanar da ayyuka na ci gaban kasar Iran a cikin shekaru 8 da ya kwashe yana shugabancin kasar, tare da jaddada cewa ci gaban da kasar Iran ta samu a lokacin shugabancinsa sakamako ne na himma da kuma kokarin al'ummar kasar baki daya.

1261641







captcha