IQNA

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Zai gabatar da jawabi a daren yau

17:37 - July 24, 2013
Lambar Labari: 2566658
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da wani jawabi a yau bayan shan ruwa, inda zai bayyana matsayin kungiyar da kuma yadda take kallon manufar kudirin tarayyar turai a kanta.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da wani jawabi a yau bayan shan ruwa, inda zai bayyana matsayin kungiyar da kuma yadda take kallon manufar kudirin tarayyar turai wannan jawabi na Sayyid Nasrullah zai zo ne kwanaki biyu bayan kudirin da tarayyar turai ta amince da shi ne da ya saka kungiyar cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Jim kadan bayan fitar da wanann kudiri dai kungiyar ta Hizbullah ta fitar da wani bayani da ke cewa, kudirin tarayyar turai da ya saka ta a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda hakan ba shi da wata kima, domin kuwa kudiri ne na siyasa da haramtacciyar kasar Isra'ila ta shirya ta mika wa tarayyar turai, ita kuma ta amince da shi bisa matsin lambar Amurka.
Bayanin ya ce babu wani abu wai shi bangaren soji na kungiyar Hizbullah, domin kuwa kungiyar Hizbullah kungiya daya ce mai yaki da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi.

1263298




captcha