IQNA

Ministan hakokin wajen Syria ya ce kudirin turai kan Hizbullah Hidima ce ga Isra'ila

17:38 - July 24, 2013
Lambar Labari: 2566659
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da yin Allawadai das aka sunan kungiyar Hizbullah a cikin jerin kungiyoyi yan ta'adda da kungiyar tarayyar turai ta yi tare da bayyana haka a matsayin hidima ga haramatacciyar kasar Isra'la.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministan hakokin wajen Syria Walid Mu'allim ya ce kudirin turai kan Hizbullah Hidima ce ga Isra'ila da ma makiya al'ummar larabawa, yayin da a na bangaren shugaban kasar Lebanon M. Sulaiman ya kirayi kungiyar tarayyar turai da ta sake yin nazari kan matakin da ta dauka, na saka abin da ta kira bangaren soji na kungiyar Hizbullah a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
A nata bangaren kungiyar ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wani bayani da ke cewa, kudirin tarayyar turai da ya saka ta a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda hakan ba shi da wata kima, domin kuwa kudiri ne na siyasa da haramtacciyar kasar Isra'ila ta shirya ta mika wa tarayyar turai, ita kuma ta amince da shi bisa matsin lambar Amurka da sauran makiya.
Bayanin ya ce babu wani abu wai shi bangaren soji na kungiyar Hizbullah, domin kuwa kungiya daya ce mai yaki da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar musulmi, tare da kore duk wata farfaganda da ke cewa kungiyar ta mallaki kamfanoni ko wuraren kasasuwanci ko kudade ko makamai a wasu kasashen ketare, inda bayanin ya ce duk wannan na daga cikin makircin da ake kitsa wa kungiyar, ta hanyar haratacciyar kasar Isra'ila da Amurka da kuma hadin baki da wasu gwamnatoci na kasashen waje.
1263105








captcha