IQNA

An Fara Gudanar Da wata gasar Karatun Kur'anI Mai Tsarki A Kasar Guinea Conakry

18:05 - July 27, 2013
Lambar Labari: 2567643
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wata gasar karatun alkur'ani mai tsarki a kasar Guinea Conakry tare da halartar malaman addini da kuma daliban makarantun Islamiyya na fadin kasar domin albakar watan Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto faga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka an fara gudanar da wata gasar karatun alkur'ani mai tsarki a kasar Guinea Conakry tare da halartar malaman addini da kuma daliban makarantun Islamiyya na fadin kasar domin albakar watan Ramadan mai alfarma da musulmi suke neman kusanci da Allah a cikinsa.

A wani labarin an daban kuma ma'aikatar shari'ar kasar Guinea Conakry ta sanar da cewar ta fara gudanar da bincike kan musabbabin bullar rikicin kabilanci da ya lashe rayukan mutane akalla 54 a yankunan da suke kudu maso gabashin kasar.
Kakakin ma'aikatar shari'ar kasar Guinea Conakry Muhammad Bouwighi a yau Laraba ya bayyana wa manema labarai cewa; an fara gudanar da bincike kan musabbabin bullar rikicin kabilanci da ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu masu yawa musamman a garin Nzerekore da kauyukan Beyla da kuma Koule da suke kudu maso gabashin kasar Guinea Conakry.
Muhammad Bouwighi ya kara da cewar manufar gudanar da binciken ita ce gano hakikanin abin da ya faru tare da hukunta mutanen da suke da hannu wajen kara ruruta wutar rikicin, kuma a halin yanzu haka jami'an tsaron kasar suna tsare da wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.
Tun a ranar Litinin 15 ga wannan wata na Yuli ne rikicin kabilanci ya kunno kai a yankunan da suke kudu maso gabashin kasar Guinea Conakry, inda rikicin ya lashe rayukan mutane akalla 54 tare da jikkata wasu fiye da 160 na daban.
1264181
captcha