Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, A yayin ganawar wacce aka fara ta tun da misalin karfe biyar na yamma har zuwa lokacin sallar magariba (kimanin karfe 8:30), wasu daliban jami'an da wakilan kungiyoyi daban-daban na daliban jami'oi su 12 sun gabatar da jawabansu inda suka yi bayani mahangarsu kan batutuwa daban-daban da kuma matsalolin da daliban jami'oin suke fuskanta.
A nasa bangaren, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya yi karin haske da amsa wasu tambayoyin da daliban jami'oin suka gabatar da kuma bayyanar da mahangarsa kan batutuwa daban-daban da suka taso da su, kamar yadda kuma ya yi karin haske kan nauyin da ke wuyan daliban jami'oin da kuma hanyoyin da za a bi wajen kara karfafa ayyukan ilimi da yunkuri da nishadin daliban jami'an.
A jawabin nasa, Jagoran ya mika godiyarsa ta Allah Madaukakin Sarki dangane da sake samun damar ganawa da daliban jami'oin inda ya bayyana mahanga da kuma abubuwan da daliban suka gabatar a matsayin batutuwa masu kyaun gaske don haka ya kirayi cibiyoyi daban-daban na gwamnati wadanda abubuwan da aka fadin ya shafa da su dau matakan da suka dace wajen ganin an aiwatar da su.
Yayin da yake amsa tambayar wani dalibin da ya bukaci sanin irin mu'amalar da ya kamata al'ummar Iran su yi da sabuwar gwamnatin kasar, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Kamar yadda na sha fadi ne dangane da dukkanin gwamnatocin, wajibi ne a taimakawa wannan gwamnatin ma. Jagoran ya ci gaba da cewa: Wasu suna fadin cewa idan har gwamnati ta kasance kaza, to za mu taimaka mata, idan ba haka ba za mu ci gaba da sukanta. To ni dai ba na adawa da suka, to amma da farko dai akwai bambanci tsakanin suka da kuma neman aibi. Na biyu kuma wajibi ne a ba da damar yin aiki tukun. Jagoran dai ya ce shugabancin kasa wani aiki ne mai wahalar gaske yana mai cewa babu wani mutum da ba shi da rauni, don haka bai kamata a sanya dukkanin fata sama da irin karfi da ake da shi ba. Har ila yau kuma Jagoran ya yi kiran al'ummar da suka hada karfin su waje guda don magance matsalolin da ake fuskanta.
Yayin da yake amsa tambayar wani dalibin dangane da irin matsaloli da kiyayyar da ake samu tsakanin daliban jami'oin saboda sabanin ra'ayi na siyasa da kuma fahimta, Ayatullah Khamenei ya kirayi daliban jami'oin da kada su bari sabanin ra'ayi da fahimta su zamanto wata hanyar da haifar da kiyayya da fitina a tsakaninsu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda Imam ya ke fadi, ku zamanto kamar daliban makarantun addini, ta yadda a lokacin tattaunawa ta ilimi ku ba da dukkanin himmarku, amma a sauran lokuta kuma ku zamanto abokan juna.
Yayin da ya ke magana kan abubuwan da daliban jami'an suka tayar dangane da fitinar da ta faru bayan zaben shugaban kasa a shekara ta 2009, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Yayin da ake magana kan wannan lamari mai bakanta rai da ya faru, batu na farko mai muhimmanci shi ne yin karen tsaye ga doka lamarin da cutar da kasar nan ta Iran.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Ku san da cewa idan da ba don taimakon Ubangiji ba, to da ba a san irin matsalolin da wannan fitina da ta faru a shekara ta 2009 za ta haifar ba.
Yayin da yake magana kan abubuwan da suka faruwa a wasu daga cikin kasashen larabawa na rikice-rikice da zubar da jinin juna kuwa, Jagoran cewa ya yi: Wadannan abubuwan da suke faruwan, wasu abubuwa ne da suke nuni lalle an samu farkawa ta Musulunci a wadannan kasashen, to amma gazawa ta jagoranci da aka fuskanta ne ya haifar da abubuwan da suke faruwar. Ko shakka babu abin da ke faruwa a kasar Masar lamari ne mai sosa rai.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Dubi cikin abubuwan da suke faruwa a yankin nan, abubuwa ne suke tabbatar da irin karfin da tsari da siyasar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta rika ne.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Manufar marigayi Imam Khumaini ita ce tabbatar da irin wannan karfi da kuma siyasa (ta karfafa al'ummar musulmi) wadda a halin yanzu ma'abota girman kan duniya suke ta kokari wajen fada da hakan, duk kuwa da cewa ba za su yi nasara ba.
Yayin da ya koma kan kokarin da makiya Musulunci suke yi wajen haifar da sabani da kuma kiyayya tsakanin Shi'a da Sunna, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Suna ci gaba da kashewa da cutar da ‘yan Shi'a a bangarori daban-daban, saboda suna tunanin cewa ‘yan Shi'a wani sansani ne na Jamhuriyar Musulunci. To sai dai kuma makiyan sun gagara fahimtar cewa a da dama daga cikin kasahsen duniya, ‘yan'uwanmu ‘yan Ahlussunna da dukkan karfinsu suke goyon bayan tsarin Jamhuriyar Musulunci.
1265290